Sin za ta maida martani kan wasu jami’an Amurka

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce ƙasar sa za ta aiwatar da matakan hana wasu jami’an ƙasar Amurka Visa, wadanda suka ƙirƙiri karairayi, masu alaƙa da zargin keta haƙƙoƙin bil adama, tare da sa ƙaimin sanya takunkumi ga ƙasar Sin, da illata moriyar ƙasar.

Wang ya bayyana hakan ne, a yayin taron manema labarai na jiya Alhamis, bayan da Amurka ta bayyana aniyar sanyawa wasu jami’an ƙasar Sin takunkumin hana Visa, bisa fakewa da zargin keta haƙƙin bil adama.

Jami’in ya ƙara da cewa, Sin ba za ta taba amincewa da irin waɗannan matakai na keta dokokin ƙasa da ƙasa, da ƙa’idojin cuɗanyar ƙasashen duniya ba.

Don haka dai, Sin ta amince da ɗaukar matakin ramuwar gayya, domin tabbatar da kare ‘yancin mulkin kan ta, da tsaro, da ci gaban moriyar ta, da kuma kare halastattun haƙƙoƙin jami’an ta. Za ta kuma ci gaba da bin dokokin ta masu nasaba da kariya daga takunkumai daga ƙetare.

Fassarawa: Saminu