Wang Yi ya yi bayani kan ganawar shugabannin ƙasashen BRICS ƙarƙashin jagorancin Xi

Daga CMG HAUSA

Shugaban kiasar Sin Xi Jinping ya jagaranci ganawar da aka yi tsakanin shugabannin ƙasashen ƙungiyar BRICS karo na 14 ta kafar bidiyo a ranar 23 ga wata. Haka kuma ya jagoranci taron tattauna ci gaban ƙasa da ƙasa a jiya tare kuma da gabatar da wani muhimmin jawabi.

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya yi bayani kan manufofin da shugaba Xi ya gabatar, da tasiri mai zurfi da za su yi ga ƙasa da ƙasa.

Wang Yi ya bayyana cewa, ganawar da ƙasar Sin ta shirya tana da babbar ma’ana ga aikin tabbatar da adalci tsakanin ƙasa da ƙasa, da sake farfaɗo da aikin raya ƙasa da ƙasa, da kuma ingiza aikin kafa kyakkyawar makomar bil Adama.

Ya ce a halin yanzu, ana ganin sabbin sauye-sauye a faɗin duniya, don haka shugaba Xi ya gabatar da dabarun ƙasar Sin, da za su wanzar zaman lafiya da samun wadata a fadin duniya. Alal misali, tabbatar da adalci domin kwanciyar hankali a faɗin duniya, da hada kai domin samun ci gaban ƙasa da ƙasa, da ingiza hadin gwiwa tsakanin ƙasa da ƙasa domin samun ci gaba tare, da tafiya da zamani domin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen BRICS, da kuma nacewa kan kwaskwarima a gida da buɗe ƙofa ga waje domin ba da gudumowar ƙasar Sin kan farfaɗowar tattalin arzikin duniya.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa