Magance cutar Sikila a Nijeriya

A Nijeriya, an ware ranar 19 ga watan Yunin kowace shekara domin tunawa da ranar cutar sikila ta duniya. Ana bikin ranar ne don wayar da kan jama’a na duniya kowace shekara da nufin havaka ilimin jama’a da fahimtar cutar sikila da ƙalubalen da marasa lafiyar da danginsu da masu kula da su ke fuskanta.

Kafin mu san ya cutar ta ke, dole mu fara sanin yadda ake kamuwa da ita. Jini wanda ake gani a zahiri idan mutum ya ji ciwo ko kuma ya yanke jikinsa yana ɗauke da abubuwa iri daban–daban, kamar su ‘plasma’, ‘Red Blood Cells’ (RBC), ‘White Blood Cells’ (WBCs), ‘Platelets’ da sauransu. Cutar Sikila ko amosanin jini tana faruwa ne idan aka samu matsala a RBC.

RBC yana ɗauke da sinadarin ‘Haemoglobin’ (HB) a cikinsa. ‘Haemoglobin’ (HB) kala-kala ne; akwai Haemoglobin A (HBA), Haemoglobin B(HBB), Haemoglobin C (HBC), da sauransu. HBA shi ne lafiyayyen haemoglobin. Sauran HB ɗin ba lafiyayyu bane.

Cutar Sikila tana xaya daga cikin cututtukan da ake iya kauce musu kafin samuwarta. Idan kuma cutar ta samu, to tana da wahalar magani.

Idan aka ce mutum na dauke da cutar sikila tana nufin mutum yana ɗauke da sinadaran haemoglobin guda biyu marasa kyau (ba lafiyayyu ba) a jikinsa. Ma’ana dai ya gaji gurɓatattun sinadaren haemoglobin daga wurin mahaifiya da mahaifi.

A yanzu haka, cutar sikila na ɗaya daga cikin cututtukan da za a iya cewa na neman zama ruwan dare, saboda yadda ake yawan samun yin aure tsakanin masu rukunin jini AS da AS ko SS da AS.

Ciwon Sikila yana haifar da illoli daban-daban, kamar;

 • Yawan rashin lafiya akai-akai kamar ciwon ƙashi, ƙirji, ciki da sauransu.
 • Shanyewar ɓarin jiki (stroke).
 • Ciwon ƙoda.
 • Rashin zuwa makaranta ko kuma yawan tangarɗar karatu.
 • Yawan ƙarancin jini.
 • Shaye-shaye.
 • Saurin mutuwa (mutuwa lokacin ƙuruciya da sauransu).

Cutar Sikila, mugun ciwo ne. Larura ce da ke raunata mai fama da ita har ma da iyalan mai fama da ita, da al’umma baki ɗaya.

Nijeriya ta fi yawan masu cutar a duniya. Bincike ya nuna cewa duk shekara ana haifar jarirai 300,000 a duniya kuma rabi daga wannan yawan a Nojeriya ake haifarsu. Daga cikin 150,000 na Nijeriya ɗin nan 100,000 ne ke mutuwa duk shekara.

Alƙalluma sun nuna cewa ma fi yawan masu cutar suna Arewacin ƙasar ne. Masana kiwon lafiya sun yi amanna cewar rashin yin gwajin jini kafin aure yana taka rawa sosai wajen haifar yara masu ɗauke da cutar Sikila a ƙasar.

Abin baƙin ciki, wayar da kai kan cutar sikila a Nijeriya ya yi ƙasa sosai. A mafi yawan al’ummomi, yawancin ’yan Nijeriya har yanzu ba su san cutar ba.

Masu fama da cutar sikila suna fara shan wasu magunguna tun daga lokacin da aka gano suna ɗauke da cutar har zuwa ƙarshen rayuwarsu.

Daga cikin magungunan akwai ‘Folic Acid’ wanda ya ke ƙara musu jini, saboda ƙwayoyin jininsu na yawan ƙarewa. Akwa kuma ‘Paludrine’ magani ne da ke kare su daga kamuwa da cutar Maleriya don tana wahalar dasu sosai idan suka kamu.

Sai maganin ‘Peniciillin V’ shi kuma aikinsa shi ne kare su daga cututtuka masu alaƙa da numfashi. Sai ‘Hydroxyurea’ wanda ya ke taimaka wa ƙwayoyin jinin siffarsu ta zama mai kyau, ya ke kuma taimaka musu wajen rage tashin ciwon. Amma yawanci ana shan shi ne ga wanda ciwon ke masa tsanani.

Yawan shan ruwa abu ne mai matuqar muhimmanci ga masu cutar sikila saboda rashin ruwa yana tayar musu da ciwon kwankwaso da na gaɓoɓi. Sannan shan ruwan na sa jini ya ƙi gudu yadda ya kamata kuma ƙwayoyin jini su ƙi wucewa cikin jijiyoyi, wanda haka ke hana ciwon yawan tashi.

Babban maganin ciwon shi ne kada ayi aure idan akwai yiwuwar a haifi ɗa mai sikila. Kuma ana iya gane haka ta hanyar yin gwajin ‘genotype’. Amma idan ciwon ya samu, to hanya ɗaya ce wadda ake iya maganin wannan cuta.

Hanyar ita ce, dashen ɓargo (Bone marrow transplant). Shi wannan dashen ɓargo yana tare da irin tasa matsalolin kuma ba ko wane lokaci ake yin nasarar warkewa ba. Sannan kuma yana da tsada matuƙa da gaske.

Ana bawa masu sikila wasu magunguna domin samun sauƙin rashin lafiya akai-akai. Shi ya sa ake so masu sikila su riƙa zuwa wajen likita lokaci zuwa lokaci koda babu abinda su ke ji na rashin lafiya.

Abin baƙin ciki shi ne, akwai rahotannin da ke nuna cewa, wasu ma’aurata kan ƙirƙira sakamakon gwajin Genotype na qarya don samun damar yin aure. Yawanci, likitoci suna ba da shawarar cewa duk wanda ke da rukunin jinin AS ya kamata ya sami abokan hulɗa mai AA don tabbatar da cewa babu ɗayan ‘ya’yansu da zai sami ciwon sikila.

Duk da shawarwari da gargaɗi, yawancin ma’aurata suna watsi da shawarar likitoci kuma har yanzu suna yin aure. A ra’ayin da aka yi la’akari, ya kamata gwamnati ta mai da shi babban laifi ga masu rukunin jinin AS da AS, SS da SS ko SS da AS su yi aure.

Abubuwan da suke tayar da rashin lafiya ga masu ciwon sikila su ne;

 1. Zafi mai tsanani.
 2. Zazzaɓi (ko na Malariya ko kuma wani abu daban).
 3. Motsa jiki mai yawa.
 4. Ɓacin rai da sauransu.

Don haka yana da kyau a kauce wa waɗannan abubuwan.

Ta haka ne muke kira ga gwamnati a dukkan matakai da su sanya gwajin cutar sikila ya zama tilas ga duk jariran da ke asibiti. Ya kamata gwajin ya zama mai isa, kyauta kuma wajibi ne ga duk ma’aurata masu sha’awar haihuwa.

Ya kamata gwamnati ta ƙara zage damtse wajen wayar da kan jama’a game da illolin cututtuka. Akwai buƙatuwar da gwamnati ta bi wajen yaƙi da cutar sikila kamar cutar kansa da ta Ƙajamau.

Wani abin takaici shi ne, mafi akasarin ’yan Nijeriya, musamman na yankunan karkara, har yanzu ba su san ciwon ba, domin da yawa daga cikin al’ummomin ba su da wuraren kiwon lafiya masu inganci.

Don haka, ya kamata gwamnati, masu zaman kansu da ƙungiyoyi masu zaman kansu su yi ƙoƙarin kafa cibiyar dashen ɓargo aqalla a dukkanin yankunan ƙasar nan.

Ya kamata gwamnati ta samar da cibiyoyin kula da gaggawa na cutar sikila da za a ware domin magance matsalolin gaggawa na cutar sikila, tare da ƙarfafawa ma’aikatan kiwon lafiya ƙwarin gwiwa da su shiga harkar kula da masu cutar sikila. Allah Ya bamu lafiya da zaman lafiya.