Sabon kocin Manchester United, Ruben Amorim zai ja ragamar wasa tara kafin bikin Kirsimeti, wanda ke fatan mayar da ƙungiyar kan ganiyarta.
Kocin ya maye gurbin Erik ten Hag, bayan da Man United ke kasa taka rawar gani a wasannin kakar bana.
Cikin wasa tara da Amorim zai ja ragamar United kafin Kirsimeti, ya haɗa da karawar firimiya biyar da Europa League biyu da kuma League Cup.
Kocin zai fara da zuwa Ipswich Town a gasar firimiya League ranar Lahadi daga nan ya karɓi baƙuncin Bodo a Europa League ranar Alhamis 28 ga watan Nuwamba.
Wasa na uku United za ta kece raini da Everton a Premier a Old Trafford ranar 1 ga watan Disamba, sannan ta je Arsenal a karawar hamayya ranar 4 ga watan Disamba.
Ranar 7 ga watan Disamba Nottingham Forest za ta je United a gasar Premier ranar 7 ga watan Disamba, daga nan United ta je ɓiktoria a Europa League ranar 12 ga watan Disamba.
Za a buga wasan hamayya tsakanin Manchester City da United ranar 15 ga watan Disamba, sai Man United ta buga League Cup zagayen kwata fainal da Tottenham ranar 19 ga watan Disamba.
Daga nan United za ta fafata da Bournemouth a Premier a Old Trafford ranar 22 ga watan Disamba.