WASIƘU: Batun aikin wutar lantarki a Mambila

Assslam alaikum! Kirana ga Gwamnatin Tarayya shi ne su ƙara himma, domin wani bincike da BBC Hausa ta gudanar ya bankaɗo cewa ba a yi komai ba a wurin da aka ware domin aikin tashar samar da wutar lantarki ta Mambila da ke jihar Taraba a Arewa-maso-gabashin Nijeriya ba shekara arba’in da fara maganar aikin.

Tun a shekarar 1982 ne lokacin mulkin tsohon shugaban Nijeriya, Shehu Shagari aka fara maganar tashar wutar wacce a lokacin aka tsara za ta samar da wuta megawat 2,600.

Gwamnatoci da suka shuɗe sun sake fasalta aikin wutar inda a shekarar 2012 ƙarƙashin shugaba Goodluck Jonathan aka ƙara yawan megawat da tashar za ta samar zuwa 3050. A ainihin gaskiya, ya kamata Gwamnati ta ƙara himman wajen ganin an fara tare da aiwatar da aikin yadda ya kamata.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa a Katsina, 07066434519/08080140820

Muhimmancin taimako

Asalamu alaikum! Godiya ga Allah Maxaukakin sarki, da ya sake ba ni damar aika wasiƙa na zuwa ga al’umma, ta wannna jarida(Manhaja) mai albarka.

A matsayinmu na mutane masu hankali, abu ne da ya kamata kowa ya gane cewa, duk wani ɗan Adam, komai muqaminsa, komai ƙarfin arzikinsa, komai ƙarfin jikinsa, yana buƙatar taimako. Idan ba ya buƙatar tallafin dukiya, to yana buƙatar wani, idan bai buƙatar wani tallafin, to ala tilas ɗinsa, yana da wata buƙatar daga ɗan uwansa mutum.

Kamar yadda al’amarin yake, Allah Ya halicci ɗan Adam ne a matsayin mai kasawa, wanda dole ne ya zama yana dogara da ɗan uwansa. Ke nan, babu yadda za a yi mutum ya rayu shi kaɗai ta karan kansa. Yana buƙatar rayuwa cikin mutane, ba dabbobi ba. Koda mutum ya yi kankanbar ƙaurace wa jama’a, ya ce zai rayu a matsayinsa na tilon mutum, to babu shakka ba zai samu dacewa da ingantattar rayuwa ba. Babu shakka zai gamu da cikas a fannoni da dama da zai fuskanta.

Ban da wannan, a kan taimaka wa ɗan Adam da sutura, domin kuwa bai zuwa da komai a jikinsa, yakan zo a matsayin tuburarre, kuma hannusa babu komai, watau fankan-fayau yake zuwa. Amma ko da iyayensa sun fi veran masallaci talauci, sai sun taimaka ma sa da suturar da za ta suturce masa tsiraicinsa.

A wannan lokacin, bai ma san inda ke ma sa ciwo ba balle ya nemi magani. Iyayen nasa ne za su yi amfani da hikima, su gano dalilin da ya sanya yake kyakyata kuka, sannan kuma su gano tare da binciko magani ko kuma mutumin da zai ba shi magani. Bayan sun samo maganin, su za su taimaka su ga cewa ya sha maganin kuma ya yi masa aiki. Wannan duk taimako ne ake yi masa, wanda idan ba a yi ba, ƙila daga nan azabar ciwo ya gallabe shi, wanda mai yiwuwa idan bai da sauran kwana gaba, sai ya koma inda ya fito.

Haka dai za a ci gaba, har yaro ya ci gaba da girma, sannan a ci gaba da ba shi abinci da abin sha da sutura. Sannan kuma a yi ta taimaka masa da huɗubobi da shawarwari, sannan ma har a sanya shi makaranta, duk dai domin ya samu cikakken hankali da halayen ƙwarai, ta yadda zai zama mai dogaro da kansa. Wannan duk wasu nau’ukan taimako ne da ake masa, waɗanda idan ba a yi masa su ba, babu yadda za a yi ya samu sa’idar rayuwa cikin daɗi.

Idan kuma ya girma, ba shi ke da dubarar samun aiki ko sana’ar da ya samu ba. Sai da ya shiga hannun wani ko wata, sannan ya koya, ya iya. Sai da aka tallafa masa, aka taimaka masa, aka ɗauke shi aiki, ko kuma aka taimaka masa da jari, sannan ya samu duk wani abu da ya samu a ma’aikatar ko kuma a wurin sana’ar tasa. Ashe lallai mutum ya samu tallafi da taimakon wasu, kafin ya samu nasara a rayuwa.

Ina fatan yanzu dai duk an gane misalaina, kuma an ankara da dalilan da ke nuna cewa mutum, ko shi wane ne, yana buƙatar taimako. Babu shakka na san yanzu an gane da haka. Idan mutum na ganin yanzu ya zama attajiri, to lallai yana buƙatar taimako ta ɓangarori da dama. Dole sai an tallafa masa kafin ya samu damar watayawa, domin kuwa akwai abubuwa da yawa da ba zai iya aiwatarwa ba da kansa. Ko da biya zai yi a yi masa da kuɗi, taimako ne dai, domin wani ɗan Adam ɗin ne zai aikata masa.

A lokacin da muka kasance attajirai, muna jin cewa lallai dukiya ba matsala ba ce a rayuwarmu. To, mu waiwaya baya mu taimaki waɗanda ba su da shi, domin mu ma an taimaka mana a lokacin da ba mu da shi. Ƙwarai kuwa, domin kuwa idan mun tuna, mu ma an taimaka mana a lokacin da mu ka zo duniya a matsayin tsirara, ba tare da komai ba a hannunmu ko a jikinmu.

Idan mulki ne Allah Ya ba ka, lallai akwai buƙatar ka yi amfani da wannan mulki domin taimakon ɗan’uwanka mutum mai rauni, domin kai ma an taimaka maka kuma akwai ranar da za ka dawo kan dole ka nemi taimakon mutane. Idan ilimi ne Allah Ya wadata ka da shi, sai ka yi himma ka taimaka wa jahilai domin su samu wannan ilimi, domin akwai lokacin da kai ma ba ka da shi, sai da wani ya taimaka maka, Domin a lokacin da ka ke jahili, wani kuwa yana da ɗimbin ilimi, sai ya taimaka maka ya koya maka wani ɓangare na iliminsa, wanda dalili ke nan ya sanya ka zama malami a yanzu. Ke nan, kwaryar da ta je, kamata ya yi ta dawo.

Idan mun lura da hikimar da ke cikin wannan rayuwar, abin ya kasance dai kamar cude-ni-in-cide-ka. Haka kuma rayuwa ta kasance tana zagayawa. Mai shi ya tallafa wa mara shi har ya zama mai shi, wanda nan gaba shi ma ya tallafa wa wani, wanda zai zama mai shi. Haka lamarin ya ke a kowa ne zamani.

Sai dai a rayuwarmu ta yau, muna ji muna gani, mun ƙeƙasar da zukatanmu, ba mu son taimako da tallafa wa juna. Wannan dalilin ne ya sanya muke cikin ruɗu da tashin hankali. Idan mai dukiya ya riƙe dukiyarsa, alhali yana ganin ’ya’yan talakawa na gararamba babu karatu, babu abin yi.

Babu shakka hankalinsa ba zai kwanta ba, domin kuwa su ne za su riƙa tare masa hanya suna yi masa kwace kuma suna razanar da iyalansa. Idan mai mulki ya ƙi amfani da mulkinsa wajen taimakawa da adalci, babu shakka shi da iyalansa da danginsa ba su tsira ba, domin dai yana zaune ne cikin mutanen da yake wa rashin adalcin. Gaskiya ya kamata mu hankalta!

Daga Mustapha Musa Muhammad a Kaduna, 08168716583.