Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Bincike ya fallasa yadda gwamnatocin jihohin ƙasar nan 30 suka kashe maƙudan kuɗi wajen sayen kayan kwalam da maƙulashe yayin taruka da tafiye-tafiyensu cikin watanni uku.
An gano cewa a cikin watanni uku kacal, gwamnonin sun kashe Naira Biliyan 986.64 domin walwalarsu yayin gudanar da taruka.
An tattaro alƙaluman ta hanyar amfani da bayanan da shafin BudgIT ke wallafawa wanda ke ɗauke da bayanan kuɗin da gwamnatoci ke kashewa a jihohinsu.
Rahotanni sun gano cewa jihohin sun kashe Naira Biliyan 5.1 wajen sayawa baƙi abin maƙulashe, inda aka ɓatar da biliyan N4.67 a matsayin alawus na zama ga jami’an gwamnati.
Haka zalika, an kashe wasu biliyan N34.63 kan tafiye-tafiye, da wasu biliyan N5.64 da aka kashe domin biyan kuɗin wuta da ruwa.
Wasu miliyoyin sun tafi ga kuɗin hawa yanar gizo, zubar da shara da makamantansu.
Ga jerin jihohin qasar nan da adadin da suka kashe cikin watanni ukun farkon shekarar nan;
- Adamawa – Biliyan N23.7
- Akwa Ibom – Biliyan N46.85
- Anambara – Biliyan N9.91
- Bauchi – Biliyan N35.75
- Bayelsa – Biliyan N35.1
- Legas – Biliyan N189.62
- Borno – Biliyan N18.79
- Jigawa – Biliyan N15.52
- Kaduna – Biliyan N34.69
- Kano – Biliyan N34.41
- Katsina – Biliyan N21.87
- Kebbi – Biliyan N11.67
- Kogi – Biliyan N37.4
- Kwara – Biliyan N24.34.
- Nasarawa – Biliyan N18.61
- Ogun – Biliyan N47.12
- Ondo – Biliyan N31.12
- Osun – Biliyan N24.39
- Oyo – Biliyan N40.12
- Filato – Biliyan N24.70
- Zamfara – Biliyan N13.46
- Taraba – Biliyan N20.93
- Abia – Biliyan N10.92
- Kuros Ribas – Biliyan N17.44
- Delta – Biliyan N68.68
- Ebonyi – Biliyan N14.95
- Edo – Biliyan N32.32
- Ekiti – Biliyan N32.8
- Enugu – Biliyan N7.51
- Gombe – Biliyan N20.89
