Adadin masu kwalara a Najeriya na cigaba da ƙaruwa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Wani rahoto na musamman da jaridar BBC ta fitar, yace hukumar hana yaɗuwar cutuka ta ƙasa, NCDC tana sanar da al’umma cewa adadin masu kamuwa da cutar kwalara na ƙaruwa a faɗin Najeriya ganin yadda damuna ke ƙara ƙamari.

Rahoton yace daga watan Janairu zuwa Yunin shekarar 2024, an samu jimillar mutum 1,141 da ake zargi da kamuwa da cutar, da 65 da aka tabbatar sun kamu da ita, da kuma 30 da suka mutu a ƙananan hukumomi 96 na Jihohi 30 sakamakon ɓullar cutar.

A kwanannan ne aka samu ɓullar cutar a Jihar Legas lamarin da ya ƙara dagula al’amura.

Jihohin da suka fi fama da cutar kuma suke bada kashi 90 na yaɗuwar ta sun haɗa da Abia da Bauchi da Bayelsa da Cross River da Delta da Imo da Katsina da Nassarawa da Zamfara da kuma Legas kamar yadda jaridar ta ruwaito.

By Babaji