Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, da Uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu sun kashe aƙalla Naira Biliyan 5.24 wajen balaguron gida da waje tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2024.
Wani bincike da aka yi ta hanyar amfani da GovSpend, wani dandalin fasaha na jama’a da ke bin diddigin yadda Gwamnatin Tarayya ke kashe kuɗaɗe, ya nuna cewa an ware Naira biliyan 1.35 don tafiye-tafiyen shugaban ƙasa da kuma abubuwan da suka shafi hakan cikin watanni uku.
Bugu da ƙari, an yi amfani da Naira Biliyan 3.53 wajen tafiya ƙasashen waje yayin balaguro 10, sannan an biya miliyan N637.85 ga hukumomin balaguro guda biyu na tikitin jirgin sama na tafiye-tafiye na gida da waje.
A baya dai shugaban ƙasar ya kashe naira biliyan 3.4 wajen tafiye-tafiye a cikin watanni shida da hawansa mulki, adadin da ya ƙaru da kashi 36 fiye da naira biliyan 2.49 da aka ware don tafiye-tafiye a kasafin kuɗin shekarar 2023.
Gabaɗaya, an kashe biliyan N8.64 a balaguron gida da waje tsakanin watan Yuni 2023 zuwa Maris 2024.
Rahoton ya kuma nuna cewa shugaban ya karɓi Naira Miliyan 650 a matsayin kuɗin kashewa.
’Yan Nijeriya dai na nuna damuwarsu kan tafiye-tafiyen da Shugaban ƙasar ke yawan yi, inda suka yi kira da a samu sakamako mai ma’ana daga waɗannan tafiye-tafiye.
A cikin watanni bakwai na farko a kan karagar mulki, Shugaba Tinubu da mataimakinsa Shettima sun ziyarci ƙasashe 16, inda su ka kwashe kwanaki 91 tare a kan harkokin ƙasashen waje.
Ziyarar ta Shugaba Tinubu ta haɗa da tafiye-tafiye guda biyu kowacce zuwa Faransa, da Bissau, Guinea-Bissau, da tafiye-tafiye zuwa Landan, Nairobi, Porto-Novo, New Delhi, Abu Dhabi, Dubai, New York, Riyadh, da Berlin, jimlar kwanaki 55.
Ƙwararre kan harkokin kuɗi Olorunfemi Idris ya bayyana cewa tafiye-tafiyen shugaban ƙasa na iya ƙarfafa hulɗar diflomasiyya, da inganta muradun ƙasa, da kuma jawo hannun jarin ƙasashen waje.
Misali, tafiye-tafiyen da Shugaba Tinubu ya yi a baya-bayan nan ya haifar da yarjejeniyoyin bunƙasar tattalin arziki, da sauyin yanayi, da kuma saka hannun jari a ayyukan more rayuwa da lantarki.
Duk da haka, Idris ya kuma bayyana tsadar waɗannan tafiye-tafiye, wanda zai iya karkatar da kuɗaɗe daga muhimman fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, da samar da ababen more rayuwa a Nijeriya.
