Tare da Bashir Mudi Yakasai
Ma’abota hikima na cewa “a-tara-a-tara ba ta hana ɓarawo sata”, saboda haka duk wata kururuwa da ’yan ƙasa za su yi, saboda ɓarayin biro da abokar hurɗarsu, wato ɓarayin zaune na gida da na ƙetare, ba za su daina ba, sai dai su fito da sababbin dabaru na duk wani tarko da aka kafa, domin wai a kama su. A taƙaicen taƙaitawa maganinsu hakunci mai tsanani, musamman hukuncin da ya ke da tozartawa, domin babu wulakanci da ɗan adam ya guda illa tozartawa domin ciwo ne da baya warkewa har abadan-abadan.
Wannan wani mubuɗi ne ga hakumomi da suke sa ido kuma suke yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ƙasa zagon ƙasa, kamar EFCC, ICPC, DSS kai da duk wata kafa da za ta toshe kuma ta hana “yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa”. A matsayin matashiya, a wannan ƙasa ta Najeriya an yi shirye-shirye managarta a lokacin fafutukar neman ’yancin kai a shekarun 1950 zuwa 1960 da fatan da kuma niyyar zama ’yantacciyar ƙasa da cigaba a dukkan fannonin rayuwa – ilimi, tattalin arziki, siyasa mai nagarta da zamantakewa mai ɗorewa.
Amma kash samun makamashin man fetur da gas a ƙasa sai ya haifar da rashawa wacce ta tunɓuke duk wani ginshiƙi da aka kafa, rashawa ta bi duk wasu jijiyoyi na alheri da suke jikin ɗan Nijeriya kamar gaskiya, amana, son ƙasa da aiki tuƙuru aka katse su ƙasa ta koma hannun ɓarayin zaune da ɓarayin biro da kuma talakawa cima zaune waɗanda cutar alaƙaƙai ta “free-syndrome” da kama su shekara da shekaru. Cuta ce mai wuyar warkewa ta na buƙatar wayar da kai kan kishin neman na kai da kishin kai da kuma kishin ƙasa. Wato, dai aikin da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, ba wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Muhammad Idris.
Allah ya jiƙan Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ba don ya mutu ba, a’a saboda hangen nesansa cewa, ’yan Najeriya na buƙatar daidaita sahunsu ta cusa kishin ƙasa da kishin kansu a zukatansu. Ba don komai ba sai abinda zai faru daga lokacin da Nijeriya ta daina dogara daga cinikin man fetur da gas wanda suka saba kwasa suna facaka su da ’ya’yansu da matansu. Daga mataki ɗaya da aka fara “cire tallafi” daga makamashin man fetur da gas da kuma sauran dangoginsa, mu ga matsalar da suka jefa ƙasa, fatara da talauci da kuma hahhawar farashi a dukkan al’amura.
Kasuwar makamashin “hydrogen” da gwamnatin Najeriya za ta shiga nan da shekara ta 2030, to, a yi taka-tsantsan tun kafin wannan lokaci, Nijeriya ta guji shiga harkar ɗari bisa ɗari ta bar wa ’yan kasuwa kashi 80, ’yan ƙasa kashi 20 baƙi ’yan ƙasashen waje. Idan ba a yi haka ba, to gaskiya idan ba a yi haka ba ba za ta sake zani ba, sai ma al’amura suke ƙara taɓarɓarewa, domin kuwa ɓarayin nan na biro suna nan kuma sun koya wa ’ya’yansu da jikokinsu. Wato dai ɓarna bisa ɓarna ta na magani shine kafa kotuna na nan take ga duk wanda ya yi almundahana da almubazzaranci da dukiyar ƙasa ya tafi lahira tare da waɗanda suka taimaka masa. Kamar yadda muka ji makamashin ‘hydrogen’ zai ba wa ’yan qasa ayyukan yi sama da miliyan 112 a tsahon wannan lokaci, kusan sama da miliyan 18 a duk shekara, wannan batu ga duk mai hankali zai ce sambarka. Matsalar wacce hanya za a bi a yi maganin waɗannan marasa kishin ƙasa da kishin bil-adama (’yan Najeriya).
Idan makamashin ‘hydrogen’ zai samar da wannan garaɓasa, me hasken rana da iska za su bayar a matsayin su na makamashi da duniya take bukata yau da kullum kuma ba su da wani haɗari na gurɓata mahalli. Mu yi taka-tsantsan da ƙasashen Turai da tsare-tsarensu da kuma shawarwarinsu, tarko ne da zai kora mu mu faɗa wanda sai aka kwashe shekaru ɗari ba mu fita ba, kamar yadda jiga-jigan kamfanonin man fetur da gas da kuma dangoginsu suke takawa a Nijeriya daga 1953 zuwa yau, 2024, wato shekaru 71 kenan. Ka yi tambaya su wa ke da riba?
Mu yi taka-tsantsan da zuwan Jamus dangane da makamashin ‘hydrogen’, babu tantama makamashi ne maras haɗari ga kewayen ɗan adam, wato muhalli, amma wa yake da iko wajen sarrafa shi? ’Yan kasuwar Najeriya ko kuma na ƙasar Jamus, idan har Jamus ce to, babu shakka su ne da riba ba Nijeriya, mu za mu zama ’yan kallo, kamar yadda matatun man fetur na qasa suka gaza aiki, bayan duk na ƙasashen Afrika da sauran duniya na aiki. A bar mutane ’yan ƙasa kamar yadda tsohon Shugaban ƙasa ya ba wa kamfanin Dangote, tunda akwai kamfanoni da ake yaqi da su da ake kira “haramtattan matatun man fetur a jihohin Delta da Rivers da kuma Bayelsa”.
Shawararmu ga gwamnati ta Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Sanato Kashim Shatima Mustapha, ita ce, su ɗaura ɗamara da Attajiran Najeriya da abokansu na cikin gida da su kakkafa masana’antu na samar da wannan makamashi na ‘hydrogen’ da kuma kasuwarsa a duk faɗin ƙasar nan. Kuma a ba su dama su yi takara da makamashin da sababbin motocin gwamnati za a fara amfani da su a wannan shekara marasa amfani da man fetur.
Za mu ga amfanin haka a lokacin matatar man fetur ta Dangote ta fara fitar da man dizal akan farashin Naira 1680 a kowacce lita, amma da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanya baki nan take Aliko Dangote ya sako da farashin zuwa Naira 1000, ba tare da wani kace-nace ba. Shi ya sa muke kira da gwamnatoci tun daga ƙananan hukumomi, jihohi har zuwa babbar giwa, Gwamnatin Tarayya, da su guji shiga harkokin kasuwanci aikinsu lallashin mutanensu da su shiga irin wannan kasuwanci, domin kuwa Nijeriya babbar kasuwa ce, inda mutum sama da miliyan 250 suke rayuwa a cikinta.
Ba za mu gaji da faɗa ba, Najeriya ta girma ta kai matsayin da za ta yi wa kanta tsarkin duk wata najasa, mu guji cewa, sai wasu daga Turai ko Amurka sun zo sannan za su gaya mana yadda za mu yi al’amuranmu, walau na ilimi, kiwon lafiya ko na zamantakewa ko na siyasa koma na tattalin arziki. Duk wani tsari da za su zo da shi tsari ne dasu suke da riba, mu ko la’ada ba sa ba mu sai kawai rarraba mu ta fuskar addini da ƙabilanci da rabuwar yanki-yanki, domin su sami saukin tatsar arzikin ƙasa da sunan dimukraɗiya.
