Wasu ’yan bindiga sun kashe junansu wajen rabon kuɗin fansa a Taraba

Wasu haɗamammun ’yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sheƙe juna a Jihar Taraba bayan da hayaniya ta kaure a tsakaninsu lokacin da suke ƙoƙarin raba kuɗin fansar da aka ba da na wani wanda suka yi garkuwa da shi.

Rikicin ya kaure ne a tsakaninsu a lokacin da suke shirin kasafta kuɗin da suka karɓa a hannun wani ɗan kasuwa da suka kama a garin Jalingo a makonnin baya.

Rahotanni sun nuna cewa, rikicin ya kaure ne a bayan wani dutse da ’yan bindigar suke ɓoyewa a kusa da wani ƙauye a Ƙaramar Hukumar Ardo Kola da ke Jihar Taraba.

Mutanen ƙauyen sun ce sun ji hayaniyar ’yan bindigar da tsakar dare a lokacin da suke faɗa da juna, da gari ya waye kuma suka tsinci gawarwakinsu a warwatse wuri-wuri.

Mutanen da ke zaune a yankin da abin ya faru sun bayyana cewa, ’yan bindigar suna zaune a ƙarƙashin dutsen, amma kuma ba su sanar da hukuma ba saboda gargaɗin da ɓarayin suka yi musu.

Suka ce, “mukan ga suna wucewa ta jikin Kogin Mallam Garba a kan babura zuwa wuraren vuyarsu amma ba za mu iya sanar da hukuma ba saboda gargaɗin da suka yi mana. A wasu lokutan mukan ga har yadda ake kawo masu kuɗin fansa a cikin dajin.”

Sai dai mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce ba su da labarin aukuwar lamarin a hukumance, saboda ya yi tafiya zuwa wani wuri a lokacin da aka yi ƙoƙarin ji ta bakinsa.

Ya ce, da zarar ya samu dawowa zai yi ƙoƙarin bincike a kan al’amarin.