Wata budurwa ta koma tsohuwa sakamakon wata cuta

Wata budurwa mai suna Raizel Calago ’yar shekara 16 ce kacal, amma ba za a taɓa tsammani shekarunta kenan ba idan aka gan ta a yanzu.

Budurwar tana fama da wata cuta da ba kasafai ake samun mutum da ita ba. Masana sun ce ana kiran wannan cuta ‘Progeria’, wadda ta ke sa yaro ruvanya shekarunsa sau huɗu ko biyar.

A cikin shekara biyu kacal, Raizel ta tashi daga kyakkyawar budurwa, wadda ta taɓa halartar gasar sarauniyar kyau, ta koma tamkar tsohuwa ’yar shekaru 70.

A yanzu halittarta ta sauya zuwa wata tsohuwa, har mutane da yawa suna kuskuren kiranta da sunan kakarta.

Matashiyar ’yar asalin ƙasar Filifin ta ce, ta fara lura da yamutsewar fatar jikinta, ’yan kwanaki sai wasu quraje suka fara fituwa a duk jikinta.

Jajayen alamomin ƙuraje suka bayyana ma ta, kuma lokacin da ta je duba lafiyarta, an gaya mata cewa ƙwari ne suka haddasa ƙurajen.

An ba ta magani, amma hakan bai yi tasiri ba, kuma ba da daɗewa ba, ta fara lura da canje-canje a jikinta.
Yanzu, yana da wahala a yi imani ita ’yar shekara 16 ce a duniya, domin wani zai iya rantsewa ya ce, shekarunta sun kai 70 zuwa 80.

Mahaifiyar Raizel mai suna Joela, ’yar sheakara 36, ta bayyana cewa, “ina jin baƙin ciki sosai idan aka gaya min cewa ’yata ta girme ni. Wani lokaci, ina tunaninta lokacin da ta tsufa kuma na ga yadda za ta yi kyau. Tana da kyau tun tana jaririya, amma yanzu fuskarta ta yi nisa da kyanta lokacin tana ƙarama.”

Tun lokacin da kamanninta suka canja, budurwar mai shekara 16 tana jin kunyar yin cuɗanya da ƙawayenta kamar yadda ta saba. Ta kuma guji fita ba tare da abin rufe fuska ba. Yawanci fuskarta a rufe yake, saboda tana jin kunyar yadda ta kasance.

Abin da kawai ta ke so shi ne jikinta ya koma yadda yake shekarun da suka gabata.