Yadda na ci kyautar da wani jarumi a Kannywood bai ci ba – Gidan Dabino

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A makon jiya mun yi muku gabatarwa kan wannan tattaunawa da Manhaja ta yi da fitaccen jarumi kuma marubuci, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino (MON), inda mu ka yi muku alqawarin cewa, a wannan makon za mu kawo muku cikakkiyar tattaunawar. Shi dai Gidan Dabino ba baƙo ba ne a masana’antar Kannywood, domin su ne suka yanke mata cibiya, ya fara da dirama ne tun a shekarar 1984, wato shekaru 37 da suka gabata, a zantawarsa da wakilin Manhaja a Kano Ibrahim Hamisu, za ku ji yadda Ado Ahmad Gidan Dabino ya lashe kyautar jarumin jarumai har sau uku a shekara ɗaya, da fim ɗaya, a fim ɗin Juyin Sarauta’ wato ‘Best Actor in leading Role. Ko a watan Nuwamban da ya gabata, Gidan Dabino MON ya samu nasarar lashe kyautar Jarumin Jarumai a gasar mawaqa da fina-finai ta Afrika ta Yamma wato West African Music and Movie Awards’ WAMMA Awards da aka gudanar a Yamai, babban birnin Ƙasar Nijar da fim ɗin Kwana Casain, a vangaren diramar talbijin mai dogon zango Best Actor in a TV Series. Ku biyo mu don jin yadda hirarsa da Manhaja za ta kasance:

Yaushe ka fara harkar Finafinan Hausa?
Na fara da wasan kwaikwayo na dave, wato ‘stage drama’ a ƙungiyar Gyaranya Drama, a shekarar 1984.

Me ya ja hankalinka ka shigo fim alhalin a rubutun littafi a ka sanka ?
Na fara harkar rubutu da kuma wasan kwaikwayo na dave a lokaci ɗaya, a shekarar 1984. Don haka ina yin su a lokaci ɗaya, daga baya kuma da fina-finan na bidiyo suka fara, na juya littafina na’ In Da So Da Kauna’ zuwa fim a shekarar 1994 ya fito a 1996. 

Harkar fim tana da faɗi. A wane ɓangare ka ke taka rawa ko ka fi ƙwarewa?
Ina rubutawa, ina shiryawa, ina bayar da umarni, ina ɗaukar nauyi, sannan ina fitowa a matsayin ɗan wasa. Ya zama abubuwa biyar nake iya yi. 

Ya zuwa yanzu fina-finai nawa ka taka rawa a ciki?
To, rawar ta kasu kashi-kashi. Ɓangaren shiryawa da bayar da umarni da ɗaukar nauyi, Kamfanina, Gidan Dabino International Nigeria Limited, mun shirya fina-finai goma sha takwas. Ɓangaren fitowa a ciki kuwa wato a matsayin ɗan wasa na fito a fina-finai sama da talatin.

Kwatsam sai aka ganka a cikin fim ɗin ‘Kwana casa’in’ a matsayin ɗan takarar gwamna har ka zama gwamna. Ta yaya ka samu kanka a shirin?
Na samu kaina a cikin shirin ne sanadiyyar an gwada wasu ba su bayar da abin da ake buƙata ba, shi ne aka sa Falalu Dorayi ya yi min magana a kan batun, da na amince zanyi aka nemi in aika da CV ɗina, bayan nan aka nemi in zo gidan TV na Arewa don a yi min ‘Audition’ (wato gwaji) saboda tsarin su ne ko dokar su ce in dai za ka taka muhimmiyar rawa a gwada mutum, na je na gwada kuma bayan wani lokaci aka kira ni aka ce an yi na’am da gwajin da na zo na yi, ni zan zama Malam Adamu gwamnan Alfawa a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’.  

Wacce fitowa ce ta fi burge ka a fim ɗin Kwana Casa’in?
Fitowar da ta ke fin birge ni ita ce, na fita zagayen ganin ayyukan da gwamnan Alfawa ya yi a garin ko kuma zuwan ba-zata a makarantu, don a tabbatar da ana yin aiki yadda ya kamata.

Wacce irin fitowa ce ta fi ba ka wahala kafin ka aiwatar da shi?
Wajen da ‘yan dabar siyasa suke tare mu suka biyo mu da makamai suna sarar mu, mu bazama cikin daji. A wajen wasu ma sun tattaka kaya sun yi rauni. Wannan shi ne mafi wuya a wajena. 

Wasu na cewa me ya sa ba za ku bai wa matasa dama ba, su fito su taka rawa a wasu fina-finai amma ku dattijai kun babbake wurin. Me za ka ce akan haka?
Shi ya sa a lokacin da na ji ana sanarwar neman masu son su shiga cikin shirin ‘kwana Casa’in su aiko da CV ɗin su, ni ban aika ba, ban kuma nema ba ko a baki. Wato in yi wa wani maganar cewa ina son shiga. Amma ina zaune aka kira ni a waya aka nemi in yi, kuma kafin ma in amsa gayyatar sai da na gaya wa Falalu wasu abubuwa game da shigar tawa, bayan mun fahimci juna ya san tsarina sannan ya sanar da su Nazir cewa zan yi, sannan na aika wa Nazir Adam CV ɗina. Don haka babu batun wai mun babbake, ko kaɗan, wani lokacin ai labari shi ke kiran ka kamar yadda ya kira ni. Kuma in za a yi wa labari adalci kamata ya yi wannan labarin ya dace da shi a kira shi kada a sa son rai, don yin hakan shi ke sawa da ɗan kallo ya kalla sai yace wane da aka sanya a waje kaza bai dace ba. 
 
Waɗanne irin nasarori ka samu a fagen fim?
Na sami nasarori da yawa musamman ta kasancewa ta ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa wannan masana’anta, wadda take samarwa da matasa masu yawa aikin yi, sannan kuma a matsayina na marubuci wanda yake sahun farko na waɗanda suka juya littafin su zuwa fim ba don neman riba ba, sai don sha’awa da kuma ra’ayin bunƙasa adabin. Bayan haka kuma nasarar sanayya ita ma wata aba ce mai muhimmanci, mutane da dama sun san ka a kan aikinka, kuma fina-finan da na yi suna samun yabo ta ɓangaren iyaye da yayye da ‘ya’ya da jikoki, domin kowa yana iya zama ya kalla ba tare da an ce tir ba. Wannan ma babbar nasara ce wadda take ƙara wa mutum kwazo na yin abu mai kyau. 

Waɗanne irin ƙalubale ka fuskanta a Kannywood?
Kasancewar ni ba 100 bisa 100 nake a cikin harkar fim ba, don haka ba ni da wata matsala ko ƙalubele a cikinta, domin harkar wallafa da ɗab’i da tallata shi na fi yi sosai da sosai. Don haka bana zaton ina da wani ƙalubale a masana’antar a sani na dai. Wallahu a’alamu.

Ka taba cin kyautar girmamawa a finafinan da ka yi?
Ƙwarai kuwa. Ni ne na ci kyautar da wani jarumi a Kannywood bai taɓa ci ba. Na zama jarumin jarumai (Best actor in Leading Role) sau uku a shekara ɗaya da fim ɗaya (Juyin Sarauta), Sannan fim ɗin dai na ‘Juyin Sarauta’, wanda muka shirya ni da Balaraba Ramat Yakubu, ya ci kyautar girmamawa sau talatin da shida (36) kuma bai fito kasuwa ba har yanzu. A watan Nuwamban da ya gabata ma na lashe kyautar Jarumin Jarumai na Afirika ta yamma a gasar (WAMMA Awards) da Fim ɗin Kwana 90 da ya gudana a Niamey da ke Ƙasar Nijar.

Ofishin Ado Ahmad Gidan Dabino

Wane ne mai gidanka a Kannywood?
Ban da mai gida a Kannywood, sai dai abokan aiki.

Mene ne burinka a Masana’atar Kannywood?
Burina in yi fina-finai waɗanda ko bayan raina za a dinga tuna ni da alheri.

Wacce shawara za ka bai wa abokan aikinka wajen fito da ingantattun fina-finai a masana’antar Kannywood?
Kira na gare su, su kula da addininsu da al’adarsu, kuma su ji tsoron Allah a cikin lamurransu, su sani duniya ba matabbata ba ce, za a je lahira kowa zai amshi sakamakonsa da hannun hagu ko da hannun dama. Allah ya sa mu amsa da hannun dama. Amin.

A matsayinka na tsohon hannu da ka ga jiya ka ga yau, mene ne shawararka ga matasa masu tasowa a masana’antar Kannywood?
Shawarata gare su ita ce, su yi biyayya su yi haƙuri, su aikata mai kyau, kuma su dinga bibbiyar tarihin waɗanda suka zo kafin su, yaya wane da wance suka yi zamaninsu suka ƙare, sun gama lafiya ko ba su gama lafiya ba, ta yaya za su yi koyi da waɗanda suka gama lafiya, don su ma su gama lafiya, sannan ta yaya za su guji yadda wasu ba su gama lafiya ba don su ma kada su maimaita kuren da wasu suka yi.

Mun gode da amsa gayyatar mu.
Madallah, Ina godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *