Yadda na sasanta tsakanin Buhari da IBB, Ojukwu da Ekwueme – Orji Kalu

Daga BASHIR ISAH

Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana yadda ya sasanta tsakanin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida, da tsakanin Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Marigayi Alex Ekwueme waɗanda suka kasance ba su ga maciji a tsakaninsu a wancan lokaci.

Kalu ya bayyana haka ne sa’ilin da yake kore batun cewa tsohon hoton taya murnar zagayowar ranar haihuwa na Chukwuemeka Ojukwu da ya wallafa a shafinsa na facebook siddabarun haɗa hotuna ne kawai amma ba na zahiri ba ne.

Sanata Kalu wanda tsohon gwamnan jihar Abia ne kuma jami’i mai tsawatarwa a yanzu a Majalisar Dattawa, ya ce an ɗauki hoton ne tun a shekarar 2005 inda ya shirya wata haɗuwar sulhunta tsakanin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Ibrahim Babangida da Shugabs Muhammadu Buhari da Alex Ekwueme da kuma Ojukwu.

Jaridar PlatinumPost ta ruwaito cewa, kalu ya wallafa hoton ne a ranar Alhamis da ta gabata, mai ɗauke da tsohon shugaban Biafra da Buhari da Babangida sai kuma Kalu.

Masu amfani da facebook sun tafka muhawara mai zafi a kan hoton inda wasunsu ke ganin cewa hoton ba na zahiri ba ne, siddabarun gama hotuna ne kawai.

Sai dai Kalu ya maida martani inda ya ce hoton na zahiri ne, kuma a gidansa aka ɗauka a 2005.

“A 2005 aka ɗauki wannan hoto a gidana da ke Igbere a lokacin da na karɓi baƙoncin shugabannina don sulhunta tsakaninsu, wato Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alex Ekwueme, wanda kafin sulhunta tsakanin nasu, Shugaba Buhari da Shugaba Babangida ba su magana da junansu.

“Haka ma a ɗaya ɓangaren, Dim Ojukwu Ekwueme ba su ga maciji a tsakaninsu. Sai dai ya zuwa lokacin da aka ɗauki hoton, Ekwueme bai riga ya iso ba”, in ji Kalu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *