Mahaifiyar da ta jefa ’ya’yanta a rijiya na fuskantar gwajin kwakwalwa – ‘Yan sanda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’yan sandan Jihar Osun ta bayyana cewa, Omowumi, wata mata da ta jefa ’ya’yanta biyu a cikin rijiya da ke unguwar Koledowo da ke Osogbo, na fuskantar gwajin taɓin hankali.

Rahotanni sun bayyana cewa, Omowumi ta jefa ’ya’yanta biyu, Nimisire mai shekaru biyar da Darasimi mai shekaru takwas a cikin wata rijiya da ke kusa da gidanta a ranar Litinin.

Da yake magana da City Round, mai magana da yawun rundunar, Yemisi Opalola, ya ce, wadda ake zargin bayan kama ta, an miƙa ta ga likitoci domin a yi ma ta gwajin taɓin hankali.

Opalola ya ƙara da cewa, sakamakon gwajin zai tabbatar da matakin da ’yan sanda za su ɗauka na gaba.

Ya ce, “har yanzu wadda ake zargin tana hannun ’yan sanda. Mun kai maganar wurin likitan mahaukata domin mu iya sanin halin da ta ke ciki. Mutane sun ce ba ta da hankali amma dole ne mu yi ma ta gwajin kwakwalwa mu tabbatar.”

A halin da ake ciki dai an tsinci gawar mutanen biyu daga rijiyar.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa, wasu Hausawa biyu ne da ke yankin suka tsinci gawar mutanen a ranar Alhamis.