Waye ba ya busa wiwi?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ba mamaki wannan tambaya ta ‘waye ba ya zuƙar tabar wiwi?’ ta zama bambaraƙwai don masu sha sun san kansu, haka nan kuma waɗanda ba sa busawa za su ce ina ruwan biri da gada. Kazalika ba na nufin jam’in cewa duk mutane su na zuƙar wiwi ko akasarin jama’a na hulɗa da ita ba, a’a taken ALKIBLAR wannan makon ne da ya shafi mutane da yawan gaske. Tun ban fara rubuce-rubuce ba na ke cin a na cewa wane ya cake ko wane sai da kori aljanu kafin ya fito idanun sa wuri-wuri ya yi rashin mutunci a wajen taro ko a wani waje da a ke son halin ‘yan sholisho, caburos ko duniya hayaƙin taba.

Akwai masu muƙaman gwamnati na aiki, siyasa ko ma sarautar mulkin mulukiyya da kan zuƙi wiwi don hakan ya agaza mu su su yi rashin mutunci, izgilanci ko faɗar abun da su ka ga dama ba tare da jin ko gezau ba. Yau ai wasu ko a ba a faɗa ma ka ba kai ko daga kallon idanunsu kasan akwai hayaƙin wiwi a ciki. Haka kawai za ka mutum ya rikice ya na zunduma ashar ko ya fatattaki jama’a daga gidansa amma sam bai damu da illar hakan ba. Haƙiƙa akwai tsohon gwamnan da ke zage mutane tas ya kore su daga gidan gwamnati wai shi ranar ba a daidai ya ke ba.

Kuma wani abun dariya in irin waɗannan mutanen su ka riga mu gidan gaskiya, waɗannan da su ke cin zarafi ne za su taru su kai su makwancin da ba tabar wiwi. Kuma ranar ko mutum ya na daidai ko ba ya daidai ba sauran izgilanci. Duk da haka wannan matsala ta shafi kowa da talakawa da masu hannu da shuni. Mata da maza. Sojoji da ‘yan sanda har ma za a iya samu a cikin jami’an gidan yari, shin za ka yi mamakin samun tantirin mai zuƙar wiwi a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA)?.

Shugaban hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, Burgediya Janar Buba Marwa ya ce, yawan masu zuƙar tabar wiwi a Nijeriya sun fi jama’ar Benin, Portugal da Girka yawa. Marwa na son kwatanta yadda lamarin ya yi muni ne don mutane su fahimta, don amfani da kalmar mutane da yawa ko ɗimbin jama’a na zuƙar tabar ba zai fito da hoton matsalar don kowa ya gane ba.

Ni kai na zan iya yarda don zai yi wuya na fito daga gida ban ji ƙaurin tabar wiwi ya bugi hanci na ba. Kama daga cikin banɗaki, cikin kwarurruka da duhuwar bishiyoyi masu zuƙar kan yi lib su na shan kayansu don wai su ji garas idon su ya bushe su iya samun nishaɗi ko damar aikata abun da su ka ga dama ba tare da jin kunya ba.

Benin na da kimanin mutum miliyan 12.1, Portugal na da miliyan 10.1 yayin da Girka ke da mutum miliyan 10.7. Kun ga za a iya samun jiha ɗaya a Nijeriya da ke da mutanen da su ka wuce na irin waɗannan ƙasashe. Nijeriya na da fiye da mutum miliyan 200 kuma a kowane gari akwai masu zuƙar tabar wiwi. Ai an sha kama buhuna cike da tabar wiwi da dillalai ke sayarwa. Kuma fa wacce a ka kama ne, don tabbas wacce ba a kama ba na da yawan gaske. Hakanan matsiyatan masu zuƙar ta a lunguna a kan kama, amma manyan jami’ai ‘yan jari hujja da ke sha a gidajen sama, ba mai kama su bare a je ga maganar gano masu kawo mu su tabar.

Marwa ya ce, zai yi wuya masu son a kafa dokar halalta shan wiwi su yi nasara don illar tabar na da munin gaske. Ma’ana don ganin yawan masu shan tabar, an samu wasu na ba da shawarar a halalta ta kamar tabar sigari sai dai a yi gargaɗin irin illar da ta kan haifar wa lafiyar mai sha. Tun da duk da illar taba sigari a kan keɓe wajen da masu shan ta za su je su sha duk da ba sa bin dokar. Abun haushi ma ku na tafiya a mota sai ka ga mutum ya kunna dama ya bule sauran jama’a don ya na ganin ya buɗe tagogin motar, sai hakan ya sa hayaƙin ma ya yaɗu a cikin motar, ta yadda waɗanda ba sa busawa su ma sai sun shaƙi hayaƙin.

Wata illar ma sai ka tsaya daf da mai shan taba musamman a masallaci inda a ke son haɗa sahu za ka kasa samun natsuwa sai ka haɗa da korar shaiɗan. Don haka har dai za a halalta shan wiwi to mutane da dama da ba sa sha za su iya shiga maye ba tare da niyya ba. NDLEA ta ce ba za ta daina yaƙi da shan wiwi ba wai don a na amfani da tabar don lamuran magani ko don wasu sun yi nisa wajen shan tabar.

Hulɗa da wiwi ga masu hannu da shuni ko muƙami na da sauƙin rufin asiri don za su zuƙa su ƙwama bakin gilashi kuma da ya ke ba talauci su fito ofis su cigaba da gasa jama’a. Gaskiya a ɓangaren talakawa musamman matasa, tabar ba ta yi mu su da kyau, don ba ya ga talauci da rashin tarbiyya, tabar kan zauta su har ta kai ga su na ganin tamkar za su faɗa rami ne alhali su na tafiya ne kan doron ƙasa.

Wani za ka ga ya daka tsalle wai zai tsallake rami alhali a kan shararrar hanya ya ke takawa. Na samu labarin matashin da ya tsuguna gaban tumak ya gaishe su don tunanin jama’a ce mai daraja. Irin wannan sakarci kan sa a ce wai wasu ai tabar kan sa ladabi da biyaiya amma na banza ai. Ya kamata mutane masu hulɗa da tabar wiwi su faɗakar su daina ko kuma su san dabarar da za su yi in sun zuƙa su kaucewa shirme ko wulaƙanta jama’a. Hakanan masu rabewa a lungu su turara anguwa da hayaƙin tabar akwai ɗaukar alhakin jama’a.

Ba zan kammala wannan rubutu ba tare da jan hankalin jami’an da a ke zargi da shan tabar su daina ba ko kuma in ba za su daina ba su guji zargin mai dokar barci ya buge da gyangayɗi, wato kar ya zama sun kwace tabar sannan su zaga su shanye ta don su na ganin sun fi ƙarfin doka. Wato ko ba kama suna in ka kalli wani jami’i da kyau ka san ƙasurgumin ɗan wiwi ne. Wannan damuwa ta sa yaƙin ba ya nasara sai dai a labaru ka ga an nuna an Kama buhun tabar kaza a gari kaza.

Kazalika akwai buƙatar wayar da kan jama’a musamman a kafafen labarun gargajiya kan illar zuƙar tabar don saƙon ya isa lungu da saqo na ƙasar nan har ma da ƙetare. Tsayin daka kan wayarwar zai taimaka wa matasa da ba su shiga ɗabi’ar ba su nesanta kan su da ita. Waɗanda su ka fi ban tausayi su ne mutanen mu na yankin karkara da wasu daga matasan su da kan shigo bariki kan ɗaukar zuƙar sigari zuwa ga wiwi ko shisha wayewa ce, don haka duk mai sha shi ne ɗan birni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *