Wazirin Hausawan Abuja ya buƙaci Tinubu ya rage farashin kayan abinci

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wazirin Hausawan Babban Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Ibrahim Mohammed Kamba, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya rage farashin kayan abinci domin rage raɗaɗin da talakawa ke ciki.

Kamba wanda ya yi wannan kiran a wata hira da manema labarai a Abuja kan halin da ƙasar ke ciki, ya kuma roƙi shugaba Tinubu da ya rage farashin man fetur.

Ya kuma buƙaci Tinubu da ya samar wa jama’a taransfomomi masu kyau a matakin farko domin bunƙasa wutar lantarki, ya ƙara da cewa jama’a daga lunguna da saƙo na ƙasa ba su da ingatattun hanyoyin sufuri.

Daga nan sai ya buƙaci Tinubu da ’yan majalisar dokokin Nijeriya da su samar da shugabanci mai ma’ana da zai iya biyan buƙatun ‘yan Nijeriya, tare da bayyana cewa talakawan Nijeriya na shan wahala matuƙa.

Waziri Hausawa Abuja, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ba da gudunmawar su domin ci gaban ƙasa.

By ukarofi