Wike bai taimake ni a zaɓen Shugaban Ƙasa ba – Peter Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi, ya zargi gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da ƙin taimaka masa.

Obi wanda ya zanta da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, ya kuma yi zargin an tafka maguɗi a sakamakon zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a Ribas, inda ya bayyana cewa ya yi nasara a jihar.

A Ribas, Bola Tinubu na Jam’iyyar APC, ya samu nasara da ƙuri’u 231,591 yayin da LP ta samu ƙuri’u 175,071.

Obi ya ce mutane sun zaɓe shi ba tare da la’akari da ƙabilanci ba, amma bisa ga asalinsa, ya ƙara da cewa ya ma samu ƙuri’u daga ‘yan asalin Legas fiye da na baƙin haure.

“A yankin Kudu maso Gabas ma haka lamarin yake, mutane sun san ni, mutane sun san abin da na tsayawa a kai, mutane sun san na cika alƙawuran da na ɗauka. Mutane sun san cewa na kiyaye abin da na faɗa.”

A halin da ake ciki kuma, a kwanan baya Wike ya ce Obi ne gwarzon zaɓe, yana mai cewa mulki zai ci gaba da wanzuwa a Arewa idan shi (Obi) bai tsaya takara ba.

Wike, wanda ya yi jawabi ga ‘yan kasuwar ƙabilar Inyamurai a wani ɗakin taro na garin Fatakwal a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ya ce kasancewar Obi a zaven ya tabbatar da fitowar ɗan Kudu a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

A cewar gwamnan, jihohin da Obi ya samu nasarar da Jam’iyyar PDP ta samu kuma ta bai wa Arewa damar ci gaba da riƙe madafun iko ta hannun ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar.