Wike ya roƙi ’yan Nijeriya su riƙa biyan haraji don raya ƙasa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su biya haraji, yana mai cewa gwamnati a kowane mataki na buƙatar samun kuɗi domin samar da ayyukan yi ga ’yan Nijeriya.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja, a wajen babban taron kasuwanci da zuba jari na Abuja wanda kamfanin ‘Abuja Inɓestment Company Limited’ ya shirya.

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya ce taken taron shi ne; ‘Haɓaka Zuba Jari Ta hanyar Haɗin kai’, ya dace da yunƙurin Gwamnatin Tarayya na tura ikon haɗin gwiwa don samar da damar zuba jari.

Ministan ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su daina tunanin cewa gwamnati ba ta buƙatar kuɗi.

Ya ba da misali da yadda harkokin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu suka taɓarɓare, inda ya bayyana cewa gwamnati ba za ta ci gaba da bayar da biliyoyin nairori da filaye ga masu zuba jari da ba za su iya tabbatar da ci gaban ’yan Nijeriya ba.

Kalaman ministan ya biyo bayan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na sanya harajin kashi 25 cikin 100 ga attajiran Nijeriya da ke samun Naira miliyan 100 da sama da haka duk wata a ƙasar.

By ukarofi