Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar APC ta zargi tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da tunzura al’umma kan gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu.
A yayin wata hira, mista Amaechi ya soki matasan Nijeriya na rashin yin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC na ƙasa, Festus Morka, a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana wannan kalamai na mista Amaechi a matsayin ‘rashin kishin ƙasa kuma abin takaici’.
Mista Morka, ya ce idan har dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa ɓarayi ne, to yakamata shi ma mista Amaechi a kira shi da ɓarawo domin kuwa ya riƙe muƙamai daban-daban tun daga 1999 zuwa 2022.
Ya ce ya riƙe muƙamin kakakin majalisar jihar Ribas na wa’adi biyu, gwamnan na wa’adi biyu kuma minista na shekaru 8.
Ya ce, mista Amaechi ya sha kusan dukkan rayuwarsa ne yana cin albarkacin kuɗin ƙasar nan kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka haifar da koma baya ga tattalin arziƙin Nijeriya.
“Sai dai a yanzu yana ƙoƙarin yaudarar ‘yan Nijeriya ta hanyar nuna tausayawarsa,” a cewar,Mista Morka,
Shugaban ƙasa dai na cigaba da fuskantar suka tun bayan janye tallafin man fetur da kuma karyewar darajar Naira.
Mista Amaechi ya riƙe mukamin minista na shekaru 8 a lokacin mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, amma shugaba Tinibu ya kayar da shi.
Kuma tun bayan wannan lokaci ne alaƙa ta yi tsami saboda Tinubu ya zaɓi ya yi mu’amala da Nyesom Wike wanda shi ne gwamnan a lokacin.
Bayan kuma zaɓe ne aka ayyana shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe a jihar Ribas duk da cewa Premium Times ta samu bayanan na’urar IREɓ wanda ya nuna cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 ne ya lashe zaɓen.
Abin ya ƙara tsanani ne saboda Amaechi and Wike abokan hamayya ne kuma Wike a yanzu minista ne kuma ɗan lele.
A lokaci guda kuma akwai batun rikicin Wike wanda ke iƙirarin shi ne ke jan ragamar jam’iyyar PDP a jihar da gwamnan jihar Siminalayi Fubara, wanda shi kuma ta bayyana ƙarara yana da alaƙa da jam’iyyar APP kamar yadda aka gani a zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a jihar.
Sauran mutanen da APC ta ƙalubalanta:
Jam’iyyar APC ta APC ta ƙalubalanci mutane kamar Atiku Abubakar, Peter Obi da kuma Rabiu Musa Kwankwaso, inda ta shawarci Amaechi da ya shiga cikin ‘yan uwansa da ke sukar gwamnatinsu.
Jam’iyyar APC ta ce da yawan masu sukar gwamnatinsu sun taɓa riƙe muƙamai kuma har suka gama ba tare da sun samar da wani cigaba na a-zo-a-gani ba waɗanda a yanzu suke takaicin ba sa cikin gwamnati.
