Gwamna ya dakatar da hadiminsa bisa laifin azarɓaɓin yanke sanar da ƙarancin albashi a Jigawa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna ya dakatar da mashawarcinsa bisa laifin yin furicin da bai kamata ba

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ya dakatar da mashawarcin sa kan harkokin albashi da fansho bisa laifin yin furicin da bai kamata ba.

Sakataren gwamnatin jihar Bala Ibrahim ya sanar da haka a wata sanarwaa da ya fitar a garin Dutse.

Ibrahim ya ce mashawarcin ya ce wai gwamnati ta amince a fara biyan ma’aikata da sabon tsarin mafi karancin albashi naira 70,000 a jihar

“Furicin da mashawarcin ya yi bai kamata ba musamman yadda kwamitin da gwamnatin ta kafa domin duba da bada shawara kan albashin da ya kamata a biya ma’aikata da shugaban hukumar kula da ma’aikatan gwamnati ke jagoranta ba su bada rahotanin su ba.

Ya ce a dalilin haka gwamnan ya bada umarnin dakatar da Ado har sai kwamitin da gwamnan ya kafa da ke karkashin shugabancin Atone-Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Bello Abdulkadir sun kammala gudanar da bincike.

SSG ya ce gwamnati ta bai wa kwamitin makonni biyu su gabatar da sakamakon aikin su wanda zai kunshi wanda ya yi furicin, abin da ya fada a furicin sannan da dalilin da ya sa ya yi wannan furicin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Kwamishinan yada labarai Sagir Musa, kwamishinan lafiya Abdullahi Muhammad, da babban sakataren aiyukka Muhammad Yahaya.

By ukarofi