Wutar lantarki ta ja ɓarawo ya rasu yayin sata a turansifoma

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Abiya ta tabbatar da cewa wani da a ke zargi ɓarawon kayan taransifoma ne ya rasa ransa bayan da wuta ta ja shi a ƙauyen Amoji-Ukwu da ke Ƙaramar Hukumar Obingwa a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Geoffrey Ogbonna, ya bayyana cewa, wanda ake zargin varawo ne da har ya yanke wayoyi biyu a jikin na’urar ta taransifoma da sanyin safiyar Juma’a.
Ogbonna ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a ranar Asabar a Aba.

Wani mazaunin ƙauyen Amoji-Ukwu, Chinenye Agomuo, ya bayyana cewa, an ji ƙarar fashewar wani abu a ranar Juma’a, kuma lamarin ya faru ne lokacin da wani mutum ya yanke wayoyi a jikin taransifoma.

“A safiyar Juma’a, da misalin ƙarfe 4:00 na safe, mun ji ƙarar fashewar wani abu da ake zargin na’urar taransifoma ce.

“Bayan fashewar, na fara samun kiran waya daga dan uwana da ke zaune kusa da tiransfomar, yana neman in zo wajen da abin ya faru.

“Ya ce wani ne ya hau taransifoma sai wutar lantarki ta kama shi.

“Lokacin da muka isa wurin, sai muka ga ashe matashi ne.”

Agomuo ya ce, “ya haura cikin taransifomar ne don yanke wayoyi, inda a hakan ne sai wutar ta kama shi ya mutu,” inji shi.

Ya ce al’ummar yankin sun kai rahoton faruwar lamarin zuwa ofishin ‘yan sanda na gabashin Ngwa.

Agomuo ya ce an ajiye gawar wanda ake zargin a mutuware tare da taimakon ‘yan sanda.

By Editor