Y. America da Soja Boy: Kowa ya rasa mafaɗi ya yi kuka

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ga duk masu bibiyar abubuwan da ke faruwa a kafafen sada zumunta, musamman abubuwan da suka shafi Arewa, ba zai kasa jin sabuwar dambarwar da ta ɓullo game da wasu matasa da ke tashen cin duniyar su da tsinke.

Na farko dai Y. America ɗan TikTok ne da yake sheƙe ayarsa yana maganganu na rashin mutunci da ba su kamata ba. Sakamakon abubuwan da yake yi marasa daɗi ya sa ’yan uwansa da suke damuwa da abubuwan da yake yi, kuma ana zarginsu da rashin tsawatar masa, suka je har gidansa suka lakaɗa masa duka a gaban iyalinsa. Sannan kuma suka buɗe manhajar TikTok inda yake cin kasuwarsa, suka saka shi kai tsaye yadda masu bibiyar sa za su ga abin da ke faruwa da shi, har ma suka tilasta shi ya nemi gafarar ’yan uwansa da bayyana tubansa daga baɗalar da yake yi.

Na biyu kuma, shi ne Usman Soja Boy wani fitaccen mawaƙin gambara kuma jarumin finafinai, wanda shi ma zaurukan sada zumunta suka ɗauki ɗumi game da wasu bidiyo na rawa da ya sake, inda a ciki aka gan shi yana kama ’yan matan da yake rawa da su, suna rungumar juna da wasu abubuwa da basu kamata ba. Musamman kasancewar ba a saba ganin irin haka ba a nan Arewa, inda muke da riƙo da tarbiyyar addini da kyawawan al’adu, da kuma dokokin da suka hana bayyana irin waɗannan halayen a fili. Sakamakon fitowar waɗannan bidiyoyi na abin kunya da suka karaɗe zaurukan sada zumunta, jama’a sun ta tofa albarkacin bakunansu, suna tir da abin da yake yi da sunan wayewa. 

A dalilin haka, ita ma Masarautar Marafan Sarkin Adar Gidan Igwai da ke Jihar Sakkwato, inda Soja Boy ke riƙe da sarautar Yariman Gidan Igwai, ta fitar da wata sanarwa ta musamman da ke nuna dakatarwa da tuɓe Soja Boy daga sarautarsa ta Yarima, saboda abin kunyar da yake yi, suna zubar da kimar masarautar.

Na ɗauki dogon lokaci ina wannan bayani ne domin in nuna mana irin tasirin abubuwan da waɗannan matasa suka aikata a wajen jama’a. Da kuma illar abubuwan da suka haifar na halayyar rashin tarbiyya ba su kaɗai ya shafa ba har ma da makusantansu. Kodayake matakan da aka ɗauka a kansu sun yi wa jama’a daɗi, kuma ya nuna lallai in da sauran ’yan TikTok da suke yaɗa baɗala suna rashin kunya, suna samun ’yan uwa irin haka da wasu abubuwan sun ragu. 

A wani bidiyo da wata fitacciyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya ta fitar tana jajentawa Y. America abin da ya faru da shi ya sa su sun fara tsorata da wasu ’yan uwansu da dama suke yi musu wani gani-gani. Saboda kada su ma a fara ɗaukar mataki kan shirmen da suke yi. Kodayake ita dama Murja akuyarta ta daɗe da yin kuka, sakamakon maganganu na rashin mutunci da take yaɗawa a TikTok, wanda har Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta sha kama ta kan abubuwan da take yi. 

Akwai daruruwan matasa maza da mata, musulmi ’yan Arewa, da suke yaɗa abubuwan rashin tarbiyya a TikTok, suna maganganu na fitsara, raye-raye da iface-iface iri-iri. Waɗanda aka kawar da kai daga abubuwan da suke aikatawa, ko don rashin tsayayyen mafaɗi, ko kuma don jama’a sun gaji da yi musu magana har an zuba musu ido suna aikata abin da suka ga dama. Wannan kuwa babbar asara ce, ga ɗan Musulmi a ce ya rasa wanda ya isa ya gaya masa ya ji, ko a yi masa nasiha kan abubuwan da yake yi da ba su dace ba. 

Irin waɗannan kalaman jama’a ke ta faɗa game da halin rashin ta ido da Usman Soja Boy yake nunawa, inda har yake ƙoƙarin mayar da martani ga maganganun da ake yi akan baɗalar da yake yaɗawa. Yana nuna shi neman kuɗinsa yake yi, kuma babu wata al’ada ko koyarwar addini da za ta hana shi cigaba da abinda yake yi.

Kodayake, tuni Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano ta fitar da sanarwar  dakatar da sanya Soja Boy cikin duk wani fim ɗin Hausa da waƙoƙi da za a shirya a jihar, ko kuma a yi cinikinsa a faɗin Jihar Kano. Wannan shi ma babban mataki ne da ya dace sauran jihohi ma su ɗauka. 

Yana da muhimmanci Hukumar Hisba da ke sauran jihohin Arewa su haɗa gwiwa da gwamnati da jami’an tsaro, da shugabannin masana’antar shirya finafinai da waƙoƙi, domin ganin an tsaftace wannan harka. Kuma a samar da wani tsari da zai riƙa daƙile abubuwan baɗala da ake yaɗawa ta manhajojin sada zumunta, a bisa tsarin da fasahar zamani ke amfani da ita.

Ba zai yiwu a zuba ido irin wannan rashin kunya da cin mutunci ya cigaba ba, don ko a manyan ƙasashen da suka cigaba ba sa barin ’yan ƙasar su yi amfani da zaurukan sada zumunta yadda suka ga dama ba, saboda tsaro da mutuncin ƙasar su. Lokaci ya yi da shugabanni za su nuna cewa ƙasar nan akwai doka, kuma al’ummar ƙasar nan masu kima da mutunci ne. 

Su ma ga matasan da suke aikata wannan baɗala, su gane cewa abubuwan da suke yi ba sa kyautawa, kuma saɓawa koyarwar addini ne. Sannan abin nan da suke yi da sunan ƙuruciya ko nishaɗi, ba abu ne mai kyau ba, musamman ga rayuwarsu ta gaba, da kuma mutuncinsu da na iyalinsu, domin ko sun share abubuwan da suka yi daga yanar gizo, akwai waɗanda suke taskancewa, suna ajiyewa saboda watarana.

By ukarofi