Yaɗa ilimin Musulunci ne babban aikin da ke gaban musulmin duniya —Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce babban aikin da ke gaban Musulmi yanzu a duniya shi ne yadda za su yaɗa ilimin addinin na haƙiƙa.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, bayan kammala zagaya Cibiyar Bajekolin Kayan Tarihin Annabi Muhammad (SAW) a birnin, a wani ɓangare na ziyarar aikin da ya kai ƙasar.

Ya kuma yaba wa qasar ta Saudiyya kan yadda ta samar da sabbin fasahohi na zamani da za su taimaka matuqa wajen yaɗa koyarwar addinin.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Laraba, inda ya ce, “yaɗa ingantaccen ilimin addinin zai taimaka matuƙa wajen fito da nagartattun halayensa.

“Ya zama wajibi a fahimci addinin yadda ya kamata domin sauya tunani da fahimtar mutane a faɗin duniya a kan addinin.”

Ya kuma yaba wa gwamnatin ƙasar ta Saudiyya kan gina wata katafariyar cibiya ta yaɗa addinin Musulunci, kodayake ya ce dole a sake zage damtse wajen yin hakan.

Ya ce gidan tarihin zai taimaka ainun wajen fito da kyawawan ɗabi’un addinin na ƙaunar juna, adalci da rahama da kuma zaman lafiya.

A ranar Talata ce dai Shugaba Buhari ya tafi ƙasar ta Saudiyya domin wata ziyarar aiki da kuma yin ibadar Umara ta ƙarshe a matsayinsa na Shugaban Nijeriya.