Ina raye ban mutu ba, inji Jarumi Al-Amin Ciroma, Baban Lukman

Daga BASHIR ISAH Da SANI AHMAD GIWA a Abuja

Fitaccen ɗan jaridar nan kuma jarumin Kannywood, har wa yau Kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Al-Amin Ciroma, wanda mutane suka fi sani da Baban Lukman na cikin shirin fim ɗin nan mai dogon zango, ‘Labarina’, ya bayyana cewa, yana nan da ransa, bai mutu ba saɓanin wata sanarwar mutuwarsa da aka yaɗa.

Ciroma ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyo mai tsawon daƙiƙa 46 da ya yi aka kuma yaɗa a soshiyal midiya da yammacin ranar Alhamis bayan da labarin ‘mutuwarsa’ ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda aka bayyana cewa jarumin ya yi haɗari a mota ya rasu.

Jim kaxan bayan yaxa jita-jitar ne sai jarumin ya fito ya yi jawabi ga ɗumbin masoya, ‘yan uwa da abokan arziki, da su kwantar da hankalinsu akan wannan abu da

Cikin bidiyon, an jiyo shi yana cewa, “‘Yan uwa na ji abubuwan da ke faruwa a kan wata sanarwa da aka yi cewa na gamu da haɗari kuma na rasa raina da sauransu.

“Wannan dai a zahiri ba sai na ce gaskiya ne ko ba gaskiya ba. Muna fatan Allah Ya kare mu daga irin waɗannan matsaloli da ke faruwa na masu kutse a waya da sauransu.

“Na kuma gode da addu’o’i da fatan alheri, amma ina ƙara kwantar wa mutane hankali hakan dai ba ta faru ba. Mu sha ruwa lafiya.”

Da alama dai Ciroma ya yi wannan saƙon bidiyon ne domin kore sanarwar mutuwarsa da aka yaɗa da kuma kwantar wa ‘yan uwa da masoya hankali.

Ciroma dai ba ɓoyayye ba ne a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, kuma ya jima yana bada gudunmuwa a harkar, inda ya kasance kuma ɗaya daga cikin daraktocin fina-finai, musamman a Jihar Kaduna.

Irin wannan sanarwa ta bogi aba ce da aka saba ji da gani a wannan ƙasa, musamman a kafafen sada zumunta na zamani inda akan yaɗa sanarwar mutuwar wani fitacce ko makamancin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *