An yi jana’izar Ci-garin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

An yi jana’izar ɗaya daga cikin masu riƙe da sarautar gargajiya a Masarautar Katsina, wato Alhaji Aminu Mamman Dee, mai riƙe da sarautar Ci-gari a masarautar.

Marigayin babban aminin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ne.

Tun farko an sanar da rasuwarsa da yammacin ranar Laraba, bayan fama da rashin lafiya, inda ya rasu a cibiyar kula da lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jihar Katsina.

A ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10 na safe aka yi jana’izar sa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, a fadar Mai Martaba Sarkin Katsina da ke ƙofar Soro cikin garin Katsina.

Waɗanda suka halarci sallar jana’izar sun ha’ɗa da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, Mataimakin Gwamnan jihar, Mannir Yakubu, jami’an gwamnati, Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya a Masarautar Katsina, sai kuma ‘yan uwa da abokan arziƙi.