Ya dace ƙasashen yamma su gane cewa “abun da ka shuka shi za ka girba”

Daga CMG HAUSA

Gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake ƙasar Sin ta kira taron manema labarai a yau Alhamis, inda kakakinta Xu Guixiang ya ce, a halin yanzu ana gudanar da taro na 49 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Geneva, inda akwai wasu ƙasashen dake kokarin jirkita gaskiya, da neman fakewa da batun kare haƙƙin bil-Adama a Xinjiang don su shafawa ƙasar Sin bakin fenti.

Xu ya ce, mutuntawa gami da kare haƙƙin ɗan Adam, ba maganar fatar baki ba ce, mataki ne na zahiri. Tun bayan da aka kafa Jamhuriya Jama’ar Ƙasar Sin a shekara ta 1949, ya zuwa yanzu, an samu ci gaba sosai a ɓangaren kare hakkokin dan Adam a jihar Xinjiang, baya ga dimbin nasarori da aka cimma a wannan fanni. Muna jan kunnen ƙasashen yamma cewa, akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a Xinjiang, don haka bai kamata su rika neman rura wutar rikici ba.

Xu ya kuma ruwaito wani karin magana na ƙabilar Uygur dake cewa, idan ka jefa dutse a sama, zai fada a kanka, wato abun da ka shuka, shi za ka girba, in ji malam Bahaushe.

Fassarwa: Murtala Zhang