Ƙasar Sin na ƙara ƙarfafa wa duniya gwiwa wajen farfaɗo da tattalin arziki

Daga CMG HAUSA

A wajen taro na musamman da kwamitin tabbatar da ci gaban harkokin hada-hadar kuɗi na majalisar gudanarwa ta ƙasar Sin ya shirya a jiya Laraba, an maida martani daya bayan daya kan wasu batutuwan da suka jawo hankalin kasuwannin ƙasar, ciki har da raya tatttalin arziki daga manyan fannoni, da batun kadarorin gidaje, da sauransu. Manazarta da dama sun nuna cewa, an kira taron ne cikin lokaci, wanda ya aike da wani sako a fili cewa, gwamnatin ƙasar Sin na bakin kokarinta wajen tabbatar da raya tattalin arziki bisa hasashen da aka yi, da neman jarin waje da samar da ci gaba yadda ya kamata, al’amarin da ya baiwa masu zuba jari na ƙasashen ƙetare ƙwarin-gwiwa sosai.

Kasuwannin hada-hadar kuɗi a ƙasar Sin sun fuskanci babban matsin lamba a wasu watannin da suka gabata, inda aka gano cewa, shugabannin ƙasar sun yi tunani da nazari mai zurfi game da wahalhalun da tattalin arzikin ƙasar ke fuskanta a halin yanzu, haka kuma suna da yakinin cewa, za’a shawo kan waɗannan kalubalolin.

Tun daga babban taro kan ayyukan tattalin arzikin ƙasar da aka shirya a ƙarshen bara, har zuwa rahoton aikin gwamnatin da aka gabatar a kwanan baya, raya tattalin arziki yadda ya kamata shi ne aka ba muhimmanci. Haka kuma a wajen taro na musamman da kwamitin tabbatar da ci gaban harkokin hada-hadar kuɗi na majalisar gudanarwa ta ƙasar Sin ya shirya a jiya Laraba, an sake jaddada cewa, ya dace a tabbatar da dorewar manufofin tattalin arziki.

Duk waɗannan abubuwa sun shaida cewa, tsarin hada-hadar kuɗi yana kara taimakawa ga ci gaban tattalin arzikin ƙasar Sin, da bada tabbaci ga raya tattalin arzikin ƙasar na dogon lokaci kuma ta hanyar da ta dace, kana, farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar Sin yana ƙara ƙarfafawa duk duniya gwiwa.

Fassarawa: Murtala Zhang