Ya kamata ɓangarori daban-daban su yi ƙoƙari tare don kiyaye muhallin duniya

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, kiyaye muhallin duniya, alhakin ne na ƙasa da ƙasa, kuma ana buƙatar su yi ƙoƙari tare, don tinkarar ƙalubalen yanayin duniya baki ɗaya.

Ya ce ya kamata ƙasashen da suka ci gaba, su sauke nauyin dake wuyansu na rage fitar da abubuwa masu gurɓata muhalli da cika alƙawarinsu yadda ya kamata, da samar da kuɗi da fasahohi ga kasashe masu tasowa a wannan fanni.

Kana ƙasar Sin za ta ci gaba da haɗa gwiwa da ƙasashe masu tasowa a fannin tinkarar sauyin yanayi don samar da gudummawa ga shimfiɗa duniya mai yanayi mai tsabta.

Mai fassara: Zainab