Ƙasar Sin kyakkyawa za ta ƙara damar da gudummawarta ga duniya

Daga LUBABATU LEI

Ƙarancin makamashi matsala ce da galibin ƙasashen Afirka ke fuskanta, a yayin da kuma nahiyar Afirka ta kasance ɗaya daga cikin sassan duniya da suke ƙarancin ƙarfin tinkarar sauyin yanayi, don haka, ya zama dole ƙasashen Afirka su bunkasa makamashi mai tsabta a wani ƙoƙari na tabbatar da dauwamammen ci gabansu.

A watan Afrilun bana, rukunin na’urori na farko ya fara samar da wutar lantarki a madatsar ruwa ta Zungeru da ke kogin Kaduna na Jihar Neja ta Ƙasar Nijeriya, tasha ce da kamfanin ƙasar Sin ya gina, wadda ake sa ran za ta iya samar da wutar lantarki da zai biya buƙatun birane biyu da girmansu ya kai kamar na babban birnin Abuja, wadda kuma za ta taimaka ga kyautata matsalar ƙarancin wuta da ake fuskanta a ƙasar, da ma tabbatar da dauwamammen ci gaban ƙasar.

A hakika, tuni ƙasar Sin ta aiwatar da shirye-shirye sama da 100 a fannin samar da makamashi mai tsabta da kiyaye muhalli a ƙasashen Afirka.

Misali a ƙasar Habasha, tashar Adama da ta Aysha da kamfanonin ƙasar Sin suka gina, waɗanda ke samar da wuta ta amfani da makamashin iska, sun bunƙasa makamashi mai tsabta, waɗanda suka samar da tabbaci ga bunƙasuwar masana’antu da ma rayuwar al’umma a ƙasar.

A Kenya, tashar samar da wuta ta amfani da makamashin rana ta Garissa da kamfanin ƙasar Sin ya gina, ta kasance irinta mafi girma a gabashin Afirka, wadda tsohon shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyyata ya taba bayyana ta a matsayin wadda ta taimaka wa Kenya wajen dogara da kanta wurin samar da makamashi mai tsabta.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, ra’ayin muhimmancin kare muhalli ya yi ta ƙara zame wa al’ummar Sinawa jini da tsoka. A yayin da ake kiyaye saurin bunkasuwar tattalin arziki a ƙasar, yawan iskar Carbon da aka fitar a ƙasar ma ya ragu ainun, baya ga muhallin halittu da yake dada kyautata, ƙasar Sin ta samu gaggarumin ci gaba ta fannin kare muhalli.

A sa’i daya kuma, ƙasar Sin ta yi kokarin rungumar makomar ɗan Adam ta bai daya, inda ta yi iyakacin ƙoƙarinta wajen samar da fasahohinta ga ƙasashe masu tasowa ta fuskar kiyaye muhalli.

Kawo yanzu dai, ƙasar Sin ta samar da kudi yuan biliyan 1.2 kwatankwacin dala miliyan 165 wajen aiwatar da haɗin gwiwa da kasashe masu tasowa don tinkarar matsalar sauyin yanayi, baya ga kuma daddale yarjejeniyoyin haɗin gwiwa 43 tare da ƙasashe masu tasowa 38, tare da horar da ma’aikatan kula da sauyin yanayi kimanin 2000 daga ƙasashe masu tasowa sama da 120.

Jam’iyyar kwaminis mai mulki a ƙasar Sin a babban taron wakilanta na 20 da aka kammala kwanan nan ba da jimawa ba, ta tsara taswirar gina ƙasa mai tsarin gurguzu ta zamani, inda kuma ta jaddada cewa, “ya kamata ƙasar Sin ta zamani ta kasance yadda ɗan Adam ke zaman jituwa da muhalli”, tare da tsara ayyukan da za a sanya gaba a wannan fanni.

Ban da wannan, ta kuma yi nuni da cewa, ya kamata a rungumi makomar ɗan Adam ta bai daya, “a tsaya ga kiyaye muhalli, tare da sa ƙaimin gina kyakkyawar duniyar dan Adam mai tsabta.”

Ta hakan muke iya hasashen cewa, nan da ba da jimawa ba, ƙasar Sin ba kawai za ta kasance mai ƙarfi ta fannin tattalin arziki da al’adu ba, tabbas kuma za ta kasance mai kyakkyawan muhalli.

Tabbas kuma ƙasar za ta ƙara samar da gudummawarta wajen tabbatar da kyakkawar duniyar dan Adam da ma dauwamammen ci gabansu.

Mai zane: Mustapha Bulama