Harƙallar ɗaukar ma’aikata 774,000: Sanatoci sun buƙaci sunaye da lambobin wayar waɗanda aka ɗauka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamitin Tantance Bin Ƙa’idar Aikin Gwamnati na Majalisar Dattawa na neman titsiye Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo dangane da ma’aikatan aikin leburanci 774,000 da aka ce an ɗauka aikin ƙarfi na wucin gadi cikin 2020.

A cikin 2020 ne Gwamnatin Shugaba Buhari ta fito da Shirin Musamman na Aikin Leburanci, wanda aka ɗauki matasa 1000 daga kowace ƙaramar hukuma ta ƙasar nan su 36 da Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.

An tsara cewa za su yi aikin leburanci ne iri daban-daban, har na tsawon watanni uku, inda za a riƙa biyan su Naira 20,000 kowane wata.

Sai dai kuma kusan shekaru uku bayan ƙaddamar da shirin, wasu sanatoci sun fito sun yi ƙorafin cewa babu ɗan yankin mazaɓar su ko ɗaya da aka ɗauka aikin.

Duk kuwa da cewa an amince sanatocin ne za su bayar da sunayen kashi 15 bisa 100 na waɗanda za a ɗauka aiki.

A wancan lokaci dai an samu saɓani tsakanin sanatoci da Minista Keyamo, inda su ka ce ya na da wata ɓoyayyar manufa shi ya sa ya yi kane-kane a cikin shirin.

Kan haka ne su ka yanke hukuncin cewa a maida tafiyar da harkar ɗaukar ma’aikatan a qarqashin Hukumar NDE.

Haka kuma sanatocin sun umarci a riƙa biyan alawus ɗin ma’aikatan kaitsaye a hannun NDE.

Sai dai kuma duk da haka sanatocin na zargin cewa Kiyamo bai tsame hannaye ba, domin bayan fara gudanar da shirin, ya riƙa watsa bayanan shirin a shafinsa na Tiwita.

A ranar Litinin ce Hukumar NDE ta bayyana gaban wannan kwamiti domin kare kasafin kuɗinta na 2023.

Sai dai kuma sanatocin da ke cikin kwamitin sun nuna rashin jin daɗin yadda aka yi harƙalla wajen ɗaukar ma’aikatan, har ma su ka ce ba a ɗauki ko matashi ko ɗaya ba.

Sanata George Sekibo daga Jihar Ribas, ya ce ba a ɗauki ko matashi ɗaya ba daga shiyyar ƙananan hukumomin da ya ke wakilta.

Shi da sauran sanatocin da su ka yi bayani sun ce ba a saka sunayen matasan da su ka bayar ba.

A kan haka ne Shugaban Kwamitin, Sanata Mathew Urhoghide ya bayar da wa’adin makonni biyu cewa NDE ta kai wa kwamiti sunayen dukkan waɗanda aka ɗauka tare da lambobin wayar su, sai kuma lambobin asusun bankunan su, inda aka ce an tura masu kuɗaɗen sallamar su aikin leburancin da suka yi.

Daraktan NDE Isah Abdul ya nemi a bai wa NDE makonni uku, amma shugaban kwamitin ya ƙi yarda, ya ce sati biyu sun wadatar.