2023: Idan APC ta yi nasara za a sha wahala da farko, a ƙarshe a ji daɗi – Fani Kayode

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Daraktan Kamfen ɗin Tinubu 2023, Femi Fani-Kayode, ya yi sharhi dangane da abin da ya ke nufi da cewa idan APC ta sake yin nasara a zaɓen 2023, to ‘yan Nijeriya za su ji jiki.

Ya bayyana cewa jin jikin na wani lokaci ne, amma ba mai ɗorewa ba ne, daga baya tattalin arzikin ƙasa zai gyaru, ‘yan Nijeriya su samu sauƙin rayuwa.

Da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels TV, Fani-Kayode ya ce sai an sha wahala kafin tattalin arzikin ƙasa ya gyaru.

Yana magana ne dangane da abubuwan da manufofi da ƙudirorin da APC ta ƙaddamar, na shafuka 80 mai ɗauke da ayyukan da gwamnatin Tinubu za ta yi idan har ya yi nasarar lashe zaɓen 2023.

‘Yan Nijeriya sun cika da ƙorafi, ganin cewa ƙudirorin duk yawanci alƙawurran da APC ta ɗauka ne kafin zaɓen 2023, amma ta kasa cikawa.

A cikin ƙudirorin dai APC za ta cire tallafin fetur a 2023, lamarin da a gefe ɗaya ana ganin cewa hakan zai yi maganin tulin tiriliyoyin nairorin da Nijeriya ke biya ga dillalan fetur da sunan kuɗin tallafin fetur.

A ɗaya gefen kuma ana kukan cewa idan aka cire tallafin fetur, to sai farashin lita ɗaya ta haura Naira 400.

A kasafin 2023 dai Nijeriya za ta kashe Naira tiriliyan 3.5 a watanni shidan farkon shekara wajen biyan tallafin fetur.

Sannan kuma za ta ciwo bashin Naira tiriliyan 8.2, kuma za ta biya bashin Naira tiriliyan 6.16 a cikin 2023.

Manhaja ta buga labarin da Tinubu ya ce tulin bashin da Buhari ya ciwo ba illa ba ce, duk cikin aikin ne.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa masu aibata Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa saboda sun ciwo bashi, ba su yin zurfin tunani.

Tinubu ya ce yawan bashin da Gwamantin Buhari ta ciwo ko ya ke kan ciwowa, ba illa ba ce, domin ayyukan raya ƙasa ake yi da kuɗaɗen.

Ya yi wannan furucin a lokacin da Buhari ke ƙaddamar da Kwamitin Kamfen ɗin Tinubu da Shettima a Abuja.

A wurin ƙaddamarwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa rayukan ‘yan Nijeriya za su fi garantin samun kyakkyawar kulawa a hannun APC fiye da sauran jam’iyyu masu takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke rantsar da Rundunar Yaƙin Neman Zaven Bola Tinubu, a Abuja.

Buhari ya ce ya zama wajibi a yi duk irin ƙoƙarin da ya dace domin a ga APC ta ci gaba da mulki, yadda ‘yan Nijeriya za su ci gaba da cin alherin da APC ta kawo a ƙasar nan.

Yayin da ya ke jinjina wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, Buhari ya kuma jinjina wa dukkan sauran ‘yan takarar da su ka yi zaven fidda gwani tare da Tinubu, amma su ka janye masa, ko kuma ya kayar da su.

Ya ce babu wata jam’iyyar da ta dace da ‘yan Nijeriya sai APC.

Da ya ke jawabi, Tinubu ya jinjina wa Buhari da kuma gwamnatinsa, tare da cewa idan ya hau mulki, zai ɗora daga inda Gwamnatin Buhari ta tsaya.

An dai ƙaddamar da Daftarin ƙudirorin APC, wato APC manifesto, mai shafuka 80, wanda cike ya ke da wasu alƙawurran da APC ta ɗauka tun a 2015, amma har yau ba ta cika ba.

Shugaban Kamfen ɗin Tinubu 2023, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce ya zama wajibi duk wani ɗan kwamitin kamfen ya tashi tsaye wurjanjan ya yi aiki tuƙuru.

Ya ce sai wanda aka aza ƙoƙarin da ya yi a sikeli aka ga ya yi ƙwazo, kuma ya kawo sakamako mai kyau kaɗai za a yi wa kyakkyawar sakayya idan an yi nasara.

Ya ce ba zai yiwu a naɗa ɗan kwamiti amma ya je Abuja ya yi kwance ba. Ya ce kowa ya bazu cikin karkara, domin a can ne masu zaɓe su ke. Za a yi zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.