Nan da mako guda ƙarancin fetur zai wuce, cewar IPMAN da NARTO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya da suka haɗa da ‘yan kasuwa, direbobin fasinjoji, masu ababen hawa, masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i ke ci gaba da kokawa a game da matsalar ƙarancin mai da dogayen layi da suke fuskanta idan suka je neman mai don su gudanar da al’amurran su na yau da kullum, ƙungiyar mamallakin motocin mai ta NARTO da takwararta ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu wato IPMAN sun tabbatarwa ‘yan ƙasar cewa, nan da mako guda za a kawo ƙarshen wahałar mai da ake gani a manyan biranın Nijeriya.

Tuni dai ’yan bunburutu suka fara amfani da wannan matsalar wajen cin nasu kasuwa inda suke sayar da litar man fetur a kan Naira 240 zuwa 400 a yawancin sassan ƙasar nan da suka haɗa da manyan birane kamar su Abuja, Legas, Fatakwal da dai sauransu.

Shin akwai mafita ga wannan al’amarin ƙarancin man fetur da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa musamman a makwannin baya-bayan nan, shuwagabannin ƙungiyoyin IPMAN da NARTO sun yi ƙarin bayani.

Farashin da fasinjoji masu zirga-zirga a cikin garin Abuja ke biyan direbobi ya tashi sakamakon ƙarancin man fetur da ake fuskanta kamar yadda wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja suka bayyana, inda direbobin motocin kasuwa ke alaƙanta tashin farashin da rashin samun mai a gidajen mai suna saya a wajen ‘yan bumburutu a yawancin lokuta.

A wani ɓangare kuma, hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya wato fannin Midstream da Downstream ta yi kira ga ‘yan ƙasar da kada su shiga fargaba da sayan man fetur, tana mai cewa akwai wadataccen mai a ƙasa.

Shuwagabannin IPMAN da na NARTO sun bada tabbacin cewa nan da mako guda komai zai kwaranye, za a samu mai wadataccen a ko’ina a faɗin ƙasar.

Idan ana iya tunawa dai ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu sassan ƙasar kamar su jihar Kogi a makwannin baya-bayan nan na ɗaya daga cikin dalilan da su ka jawo matsalar ƙarancin man musamman a birnin Abuja.