Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar FA ta ci tarar kocin Liverpool, Jurgen Klopp Yuro 30,00 bayan jan katin a wasan da ƙungiyarsa ta yi nasara a kan Manchester City a ranar 16 ga watan Oktoba.
An kori Klopp daga filin wasa bayan rashin ɗa’ar da ya yi wa mataimakin alƙalin wasa, lokacin da aka ƙi bai wa Mohamed Salah damar dukan da aka yi masa.
Kocin ya nemi afuwa kan halayyar da ya nuna bayan an tashi daga wasa.
“Wani abu ne ya ɗauki hankali ne, ba alfahari na ke ba. Na cancanci jan kati,” a cewarsa.
An tuhumi Klopp da karya dokar FA ta E3, wadda ta bayyana cewa faɗawa alƙalan wasa magana bai dace ba, wanda kuma ya ke janyo, wanda zai iya zama barazana da cin zarafi da zagi”.
FA ta ce, ba za a taba yarda da wannan halayyar da ya nuna ba, ba ta dace ba, kuma hukumar da ke lura da dokoki ta sa masa takunkumi da shi lokacin sauraron ƙarar.
Amma Liverpool na da damar ƙalubalantar takunkumin.