Sama da yara miliyan ɗaya za a yi wa allurar rigakafi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Aqalla ƙananan yara 1,123, 143 miliyan ne ake sa ran za a yi wa allurar rigakafin da za a yi nan gaba a faɗin Jihar Zamfara.

Mataimakin gwamnan jihar Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana haka a wani taron kwamitin yaƙi da cuttuttaka da aka gudanar a ofishin sa ranar Talata.

Mataimakin gwamnan wanda shi ne shugaban kwamitin da ke kula da harkokin rigakafi a jihar ya ce, aikin rigakafin zai mayar da hankali ne kan cutar Ƙyanda, rigakafin cutar Sanƙarau, ƙarin bitamin A, takardar shaidar haihuwa da aikin rigakafin COVID-19.

Ya bayyana cewa za a fara rigakafin ne a faɗin ƙananan hukumomi goma da suka haɗa da Bungudu, Birnin Magaji, Gusau, Zurmi, Ƙaura Namoda, Shinkafi, Talata Mafara, Maru, Tsafe da Maradun, yayin da Gummi, Bukkuyum, Bakura da Anka da sauran ƙananan hukumomin huɗu za a gudanar da su daga baya.

Mataimakin gwamnan ya ci gaba da bayyana cewa, an gudanar da taron ne da nufin cimma adadin yara 795,556 masu shekaru 5 zuwa watanni 9 da za a yi wa allurar rigakafin cutar Ƙyanda da kuma yara 327,587 masu shekaru tsakanin 10 zuwa 11 da ke da za a yi wa allurar rigakafin cutar Sanƙarau.

Ya ce yayin rigakafin, ana sa ran za a yi wa mutane kimanin 16,440 allurar rigakafin COVID-19 haka kuma za a yi amfani da ƙungiyoyi 1,092 wajen rigakafin.

Nasiha ya yi nuni da cewa tuni gwamnatin jihar ta fitar da tallafinta don gudanar da rigakafin da aka shirya gudanarwa a ranakun 27 ga Oktoba zuwa 3 ga Nuwamba.

Ya kuma yi kira ga al’umma, ‘yan siyasa, malaman addini, sarakunan gargajiya da kuma ɗaiɗaikun jama’a da su yi amfani da wannan babbar dama don tabbatar da an yi wa ɗaukacin yaransu allurar rigakafin.

Ya kuma yaba wa abokan hulɗar ci gaba na UNICEF, WHO, CDC, Chigari Foundation da Solina bisa irin taimakon da suke bai wa jihar a fannonin kiwon lafiya daban-daban, ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar ci gaba da ƙoƙarin da abokanan ci gaba ke yi na ganin an samu ci gaba don cimma sakamakon da ake so.

A jawabin maraba, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Zamfara Dr. Tukur Isma’il ya bayyana cewa manufar taron ita ce tantance ayyukan da jihar ke yi kan allurar rigakafi da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa ke yi.