Canja takardun kuɗi: EFCC za ta sa zare da masu ɓoye Naira

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati  (EFCC), ta lashi takobin sanya ƙafar wando guda da dukkan masu ɓoye Naira, a yayin da CBN ta samu sahalewar shugaban ƙasa Buhari a kan canza fasalin wasu daga cikin takardun Nairorin Nijeriya.  

Idan za a iya tunawa, Babban Banki Nijeriya (CBN) bayan samun sahalewar Buhari ya bayyana cewa, nan da 15 ga watan Disamba za ta fitar Da sabbin takardun Nairori waɗanda aka canza wa fasali. Takardun kuɗin da za a sauya wa fasalin sun haɗa da, takardun Naira 200, Naira 500, da kuma N1000.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, shi ya bayyana wannan tsarin a ranar Larabar da ta gabata, sannan ya yi ƙorafin cewa ‘yan Nijeriya sun ɓoye a ƙalla Naira tiriliyan N2.7 daga kasuwar hada-hadar kuɗi. 

Haka zalika, daga cikin Naira tiriliyan N3.3 da suke zagayawa, Naira biliyan 600 ne kawai suke a ma’ajiyar kuɗaɗen bankunan kasuwanci.  Emefiele ya ce, bai kamata haka ta dinga faruwa ba. Kuma ya shawarci ‘yan Nijeriya da su dinga ajiye kuɗaɗensu a bankuna. 

Emefiele ya ce, hanya mai kyau da Duniya ta amince da ita ce, a dinga canza kuɗin ƙasa bayan kamar shekaru biyar-biyar ko takwas-takwas. Amma kuɗaɗen Nijeriya tsahon shekaru 20 kenan ba a canza su ba. 

A cewar Gwamnan na CBN, wannan tsarin ya zama dole domin alƙalumman sun nuna cewa, kusan kaso 80 na kuɗaɗen ƙasar nan suna can a ɓoye ba a bankuna ba. 

A yayin da yake martani a kan wannan hukunci da CBN ɗin ta ɗauka, shugaban hukumar EFCC , Abdulrasheed Bawa, ya gargaɗi hukumar canji ta Nijeriya a kan su kula da mutanen da za su zo neman canji don canza haramtattu  kuɗaɗen da suka ɓoye. 

Haka zalika, Bawa ya ƙara da kira ga bankuna a kan su tabbatar sun sauke nauyinsu na  kai ƙarar duk wata hada-hadar kuɗi da ba su yarda da ita ba, da masu ajiyarsu suke yi, domin Hukumar EFCC za ta sanya ƙafar wando ɗaya da duk bankin da aka kama da karya doka. 

Daga ƙarshe, ya bayyana irin gamsuwarsa akan samar da sabbin takardun kuɗi da CBN ɗin take shirin yi. Domin a cewarsa, a kwanakin nan sun sha shiga ganawa da masu ruwa da tsaki don ganin yadda za a ɓullo wa karyewar tattalin arziki a ƙasar nan. Kuma a cewarsa, canza kuɗin wata hanya ce da za ta magance faɗuwar tattalin arzikin.