Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana buƙatar raba hanyar samar da wutar lantarki a Nijeriya don magance matsalar rushewar rumbun lantarki ta ƙasa da ake fama da ita.
A taron majalisar tattalin Alarziki ta Ƙasa karo na 145 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Shettima ya yi bayani kan matakan da za a ɗauka wajen raba hanyoyin samar da wutar, wanda ya haɗa da samar da ƙananan hanyoyin samar da wuta da kuma amfani da makamashi mai sabuntawa kamar hasken rana.
Ya kuma jaddada buƙatar gaggawa wajen aiwatar da tsarin ayyukan makamashi na Nijeriya (NESIP), inda ya nuna cewa ya zama wajibi sashen samar da wuta ya rungumi amfani da makamashi mai sabuntawa da kuma yin amfani da tsarin solar da aka tsara don biyan buƙatun wutar lantarki na yankuna daban-daban.
“Ƙarfi tattalin arziki shi ne ginshikin kowace ƙasa. Rashin wuta da aka samu a kwanakin baya sakamakon aikin masu aikata laifi ya jaddada mana buƙatar faɗaɗa hanyar samar da makamashi. Na yi imanin gwamnonin da ke nan za su yarda cewa raba hanyar samar da wuta shi ne hanyar ci gaba,” in ji Shettima.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa tsarin doka da ya bai wa jihohi damar samar da wuta, isar da ita, da kuma rarraba ta a yankunan da ke ƙarƙashin rumbun wutar lantarki ta ƙasa. Ya kuma yi kira ga sashen samar da makamashi ya rungumi amfani da makamashi mai sabuntawa domin samar da tsarin wuta mai ƙarfi wanda zai iya taimakawa al’umma.