CMG HAUSA
Qin Gang, jakadan ƙasar Sin da ke ƙasar Amurka, ya musunta yadda Amurka da sauran ƙasashen yammacin duniya suka bata sunan ƙasar Sin bisa hujjar batun ƙasar Ukraine, yayin da yake zantawa da wakiliyar CBS a ranar 20 ga wata, inda ya yi nuni da cewa, ƙasar Sin ta ki amincewa kan labarun bogi da ake bazawa, cewa wai ƙasar Sin ta samar wa ƙasar Rasha tallafin aikin soja.
Tun bayan ɓarkewar rikicin Ukraine, ƙasar Sin na himmantuwa wajen ƙara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin ɓangarori masu ruwa da tsaki, tare da gabatar da shawarwari guda 6, dangane da hana ɓarkewar ƙalubalen jin kai a Ukraine. Yanzu ƙasar Sin ta samar wa Ukraine tallafin jin kai sau da dama, tare da samar wa mazauna wurin abinci, magani, jakunan barci, madarar jarirai da dai sauransu, a maimakon samar wa Rasha ko Ukraine makamai.
Amma meye ƙasar Amurka ta yi? Bayan ɓarkewar rikicin tsakanin Rasha da Ukraine, ta yi ta hada hannu da ƙasashen yammacin duniya wajen sanya wa Rasha takunkumi daga dukkan fannoni, da samar wa Ukraine tallafin aikin soja, tana yunƙura rura wutar rikicin. Ta kuma shirya bai wa Ukraine makaman da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 800.
Amurka tana samar wa Ukraine makamai, da sanya wa Rasha takunkumi, yayin da ƙasar Sin take ƙoƙarin ƙara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha, da samar da tallafin jin kai. Kowa ya ganewa idonsa, waye ke rura wuta, waye kuma ke kiyaye zaman lafiya.
Fassarawa: Tasallah Yuan