Mutum na farko da aka yi wa dashen ƙodar alade ya mutu wata biyu bayan yi masa aikin.
Richard Slyman mai shekara 62 ya yi ta fama da ciwon ƙoda kafin a yi masa wannan tiyata a watan Maris.
Babban asibitin Massachusetts ne ya sanar da rasuwar tasa a ranar Lahadi, sai dai ba a tabbatar da ko mutuwar tasa na da alaƙa da tiyatar da aka masa.
Tiyatar da aka yi wa Slayman ta shiga tarihi, saboda yadda aka yi ta ƙalau, ba tare da samun wata matsala ba, saɓani waɗanda aka sha yi a baya.
Dama dai bayanai sun ce Slayman na fama da siga da kuma hawan jini.
A 2018, an taɓa sanya masa ƙodar mutum, amma sai ta fara ba shi matsala bayan shekara biyar.
Bayan an sa masa ta alade a ranar 16 ga watan Maris, likitansa ya tabbatar da cewa yanzu babu buƙatar a riƙa wanke masa ƙodar domin tana aiki yadda ya kamata.
Idan dai ba a manta ba, Blueprint Manhaja ta ruwaito yadda aka taɓa yi wa wani mutum mai suna Daɓid Bennett dashen zuciyar alade, inda daga baya shima ya mutu sakamakon tsayawar zuciyar da aiki.
Bennett, wanda ke fama da ciwon zuciya da ya kai maƙura ya rayu na tsawon wata biyu bayan dashen zuciyar alade da aka yi masa a Amurka.
Amma rashin lafiyar ta fara tsananta a kwanakin da suka gabata, kamar yadda likitansa Baltimore ya bayyana.
Ya ce, Daɓid Bennett mai shekara 57 ya mutu ne a ranar Litinin 8 ga watan Maris ɗin bara.
A watan Janairun da ya gabata ne mu ka ruwaito yadda Bennett da aka yi wa dashen zuciyar alade ya bayyana dalilinsa na amincewa, duk cewa ya san akwai hatsari a tattare da yin hakan.
Likitoci a aasar Amurka ne suka yi nasarar yi wa mutumin mai suna Daɓid Bennett mai shekara 57 dashen zuciyar alade da aka sauya kwayar halittarta a karon farko a tarihi.
An sanar da hakan bayan likitocin sun kammala aikin dashen zuciyar a Asibitin Koyon Aikin Likita na Jami’ar Marylanda da ke ƙasar Amurka.
Karon farko ke nan a tarihi da aka gudanar da irin wannan aiki cikin nasara a wani yunƙuri na shawo kan matsalar ƙarancin masu bayar da gudunmawa, domin ceton rayukan masu fama a matsalar zuciya.
Sanarwar da aka fitar ta ce bayan aikin da ya gudana cikin nasara, an kafa sabon tarihi a fannin yi wa ɗan Adam dashen sassan jikin dabba.
Ta bayyana cewa, an yi wa wani mara lafiyan mai suna Daɓid Bennett, dashen zuciyar aladen na bayan gwajin da aka yi masa ya nuna jikinsa ba zai iya ɗaukar dashen zuciyar dan Adam ba, saboda wasu cututtuka da ya jima yana fama da su.
An samo zuciyar aladen da aka dasa wa Mista Bennett ne daga wani garken aladu da aka yi wa sauyin kwayar halitta.
Kafin dashen, sai da aka katse wasu ƙwayoyin halitta uku da ke iya sa halittar jikin ɗan Adam kin karɓa da kuma aiki da sassan jikin alade.
An kuma katse wata kwayar halittar da ke iya sa tantanin zuciyar aladen yin girma fiye da kima.
Daga nan sai aka dasa wa zuciyar aladen wasu ƙwayoyin halitta shida da za su sa ya karɓi sassan jikin alade ya kuma yi aiki da su.
An gudanar da aikin sauyin kwayar halittar ce a kamfanin fasashar sarrafa tsirrai na Riɓiɓocor da ke yankin ɓirginia na ƙasar Amurka.
Kamfanin ne ya samar da aladen da aka yi amfani da a aikin dashen ƙodar da aka yi wa wani mutum wanda kwanyarsa ta mutu a birnin New York a watan Oktoban 2021.
A yayin da wancan aikin ya kasance na gwaji, inda aka an jona ƙodar daga wajen jikin mutumin, aikin dashen zuciyar aladen da aka yi wa Brennett na zahiri ne kuma an gudanar da shi ne domin ceton rai.
Kafin a gudanar da aikin sai da aka adana zuciyar aladen a na’urar ajiyar kayan tiyata, aka kuma sa mata wani magajin gwaji da kamfanin sarrafa magunguna na Kiniksa Pharmaceuticals ya samar, tare da wasu makamantan maganin da ake amfani da su wajen rage ƙarfin garkuwar jikin zuciyar.
Alƙaluman hukumomin Amurka sun nuna kimanin mutum 110,000 ne ke jiran a yi musu dashen zuciya, kuma sama da 6,000 daga cikinsu na rasuwa a duk shekara kafin a kai ga yi musu dashen.
