Yadda Ƙungiyar Marubutan Katsina ta gabatar da taron bita

Daga USMAN ANGO a Katsina

Ƙungiyar Marubutan Jihar Katsina da ta ke a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammad Bello Sambo ta sake gabatar da taron zaman karatu (reading sesson) karo na biyu.

Taron dai ya zo da sabon salo na ba wa marubuta da mawaƙa dama su gabatar da ayyukansu gaban ‘yan uwansu marubuta, yayin da za a yi mu su gyara da kuma jinjina.

Taron, wanda a ka gabatar a ranar Asabar, ya samu halartar wasu daga cikin jiga-jigan ƙungiyar, kamar su; Muhammad Bello Sambo (Shugaba)
Fatima S. Muhammad ( Ma’aji), Usman Ango (PRO), Abubakar Ƴar’aAdua (Baba Abu), A’isha Mobile, Lu’ubatu Isa (Ubbe), Abdulhamid M. Sani  (Malumman Matazu), Sulaiman Mangal Plaza, Shamsudden Ibrahim (Fatimiya), Ibrahim Adam Ɗan Sarauta, Malam Musa Mai Rafi Ƙofar Durɓi.

Labaran da aka karanta a wajen aka yi bitar su sun hada da;
Labari mai taken: ‘Fyaɗe’ na Hajiya Lu’ubatu Isa (Ubbe).

Labari mai taken : ‘Kamar A Mafarki’ na Sulaiman Mangal Plaza.
Labari mai taken: ‘Matsalar mu’ na Abubakar Ƴar’adua (Baba Abu).
Labari mai taken ‘Ƙaddarata’ na A’isha Mobile.

Sai waƙoƙin da aka yi sharhin su, su ne kamar haka: Ibrahim Adam Ɗan Sarauta da waƙarsa mai taken: ‘Harshen Hausa’.

Sai ta Malam Abdulhamid M. Sani Matazu (Malumma Matazu) da waƙarsa mai taken: ‘Aminina’.

Malam Musa Mai Rafi da waƙarsa mai taken: ‘Girman Allah’.

Taron ya kammala cikin nasara. Allah ya ƙara ɗaga uwa KMK.