Bai kamata ku saka mu a jerin magautanku ba – Japan ga Rasha

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin ƙasar Japan ta yi wa ƙasar Rasha ƙorafi a game da yadda ƙasar Rashan ta sanya ta a cikin jerin sunayen ƙasashen da ta ayyana a matsayin magautanta. 

Hirokazu Matsuno, Babban Sakataren ƙasar Japan shi ya gabatar da wannan ƙorafi a taron manema labarai. Inda Matsuno, ya ƙara da cewa, tabbas babban abin nadama ne a sanya ƙasar Japan a cikin magautan ƙasashe da Rasha ta yi.

Tun a ranar jajiberin taron manema labaran ne dai ƙasar Rasha ta wallafa jerin sunayen wasu ƙasashe da ta ce suna aiwatar da wasu ayyuka na nuna ƙin jini ga ita ƙasar. Inda ta jero ƙasashe kamar haka: Gamayyar ƙasashen Turai (EU), Amurka, Birtaniya da Japan da sauransu. 

A halin yanzu dai an riga an amince da dukkan dokokin hulɗa da ƙasashen waje da Rashan ta gindaya. Sannan kuma hada-hadar kamfanoni tsakanin Rasha da mutanen wasu ƙasashen ko tsakanin kamfanoni na ƙasashen magautan Rasha dole su samu sahalewa daga hukumar daidaitawa a kan harkokin ƙasashen waje.

Idan za a iya tunawa, a ranar 24 ga Fabrairun shekarar 2022 ne dai Shugaba Vladimir Putin na ƙasar Rasha ya yi amfani da ƙarfin Soja wajen yin kutse a Ƙasar Yukiren. Kodayake Vladimir Putin ɗin ya kira al’amarin da, ceto mutanen Yukiren daga qangin mulkin kama-karya da suke ciki na mulkin Kiev tsahon shekaru 8. Kuma ya tabbatar da adalci. A ta bakin ma’aikatar tsaron ƙasar Rasha, ba wani zancen mamaya tsakanin ƙasashen biyu. 

Sai dai wasu ƙasashen yammacin Duniya suna ganin abinda Rasha take a matsayin zalunci. Don haka ta ɗauki wasu salo na hukunci ta hanyar yanke hulɗa da Rashan a matsayin martani ga waccan mamaya da suka ce Rasha ta yi a ƙasar Yukiren ɗin. Misali manyan Bankunan Rasha, Sberbank da kuma VTB suna ƙarƙashin waɗannan ƙasashen ne, kuma sun dakatar da su. 

Hakazalika, Gamayyar Ƙasashen Turai da Amurka da kuma Kanada sun haramta wa jiragen Rasha daga wucewa a filayen sararin samaniyarsu da sauransu.

Ba mamaki wannan shi ne ya sa ƙasar Rasha ta fara ɗaukar matakan ko-in-kula ko kuma ko a jikina a kan waɗancan ƙasashe da take ganin sun zame mata ƙarfen ƙafa. Inda Sakataren yaɗa labaran Rasha, Dmitry Peskov ya bayyana cewa, waɗancan ƙasashen sun shirya tsaf don ganin bayan Rasha, da kuma waɗanda suka yanke ta a kasuwancinsu, Rasha a shirye take tsaf, don tura musu aniyarsu.