Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu da ake zargi hasalallun matasa ne da ke adawa da masarautar Etsu na Lokoja sun kai wa fadar Sarkin Nupe, Chief Emmanuel Dauda-Shelika, Nyamkpa Iɓ, hari inda suka ƙone kayayyaki da ke gidan da suka haɗa da wata mota.
Masarautar wacce ke gida mai lamba 306, New Layout, Lokoja, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa, NAN, an kai mata harin ne da misalin ƙarfe 1 na dare a ranar Asabar.
Wannan al’amari ya faru ne a daidai lokacin da ƙungiyar ‘yan asalin ƙabilar Nupe ke shirin gudanar da taro karo na biyu na ƙarshen shekara mai taken, “Bajekolin al’adun Nupe a Lokoja” a ranar 21 ga watan Disambar 2024.
Sai dai wannan hari da aka kawo ya dakatar da komai game da gudanar da taron.
Dauda-Shelika ya bayyana wa NAN cewa da misalin ƙarfe 1 ya ji bugun ƙofa.
“Na tashi na leƙa ta wundo domin na ga me ke faruwa. Sai na ga wuta na tashi daga cikin motata wacce har an cinna mata wuta. Don haka, na gane wannan hari ne aka kawo wa masarautar, sai na ƙi fitowa saboda ka da a farmake ni. Ta ƙofar baya na fita saobda na tsira da rayuwata.
“Bayan na fito titi ne na tarar ashe duk mutanen ƙauyen ma suna can suna ƙoƙarin kashe wuta. Amma dai an ƙone motata da sauran kayayyaki.”
Daga nan ne, Sarki ya roƙi gwamnati da jami’an tsaro ta bincika domin gano waɗanda suka aikata wannan ta’asasa da kuma waɗanda suka ɗauki nauyin harin.
Ya shawarci ƙabilar Nupe da ke Lokoja na su kauce wa kai hari inda ya hore su da rungumar zaman lafiya da zama masu bin doka da oda domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da bincike.
“Muna roƙon gwamna Ahmed Ododo da jami’an tsaro da su yi amfani da ikonsu wajen gudanar da bincike da kawo ɗaukar mataki kan waɗanda suka aikata wanann aika-aika.”
“Muna kuma roƙon gwamnati cewa da ta duba matsalolinmu da kuma ɗaga darajar wannan masarauta ta Etsu Lokoja wanda ke da daɗaɗɗen tarihi tun kafin zuwan Turawa,”
Ya kuma ce shugaban ƙaramar hukumar Lokoja tare da jami’an tsaronsa sun kawo masa ziyara domin duba irin asarar da aka yi masa da kuma ta jami’an tsaro.
Shugaban ƙungiyar ‘yan ƙabilar Nupe na Lokoja, Alh. Abubakar Ndashite, ya ce, an tsara gudanar da taron ne a ranar Asabar domin murnar ranar bajekolin al’adun Nupe amma ba ƙoƙarin naɗa kowa mulki ba.
Ndashite, wanda ke zaman shugaban ƙungiyar kuma shugaban kwamitin shirya taron, ya ce an dakatar da taron wanda ya nuna rashin jin daɗinsa saboda irin yadda ƙungiyar ta tama wa bikin, inda ya buƙaci gwamnati da ta gaggauta lalubo waɗanda suka aikata wannan ta’asa.
