Yadda aka gabatar da taron littafin waƙoƙin tambarin zamani a Kano na matashiya Salma Mailambu

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An gabatar da sabon littafin wakokin tambarin zamani, wanda matashiyar mawaƙiya Salma Saeed Mailambu ta rubuta, a wani babban taro da aka gudanar a ɗakin taro na Gidan Mambayya da ke Unguwar Gwammaja, a cikin birnin Kano, inda manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.

Taron ya samu halartar malamai, ɗalibai, masana da masu nazarin waƙoƙin Hausa da al’adun gargajiya, waɗanda suka taru domin taya mawaƙiyar murnar wannan gagarumar nasara tare da ƙarfafa mata gwiwa wajen ci gaba da ayyukan adabi.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin shirya ƙaddamar da littafin, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya yaba wa mahalarta taron bisa yadda suka nuna goyon baya tare da ba da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar gudanar da taron.

Ya ce irin wannan goyon baya na da muhimmanci wajen ƙarfafa matasa masu basira, yana mai bayyana cewa za su ci gaba da tallafa wa yara da matasa masu baiwar adabi, musamman irin su Salma.

A nata jawabin, Salma Saeed Mailambu ta bayyana cewa goyon bayan da ta samu daga iyayenta shi ne babban abin da ya ƙara mata ƙarfin gwiwa har ta kai wannan mataki.

Ta yi kira ga iyaye da su riƙa tallafa wa ’ya’yansu tare da ƙarfafa musu gwiwa domin su samu damar amfani da baiwar da Allah Ya hore musu wajen amfanar al’umma.

Littafin Tambarin Zamani ya ƙunshi wasu daga cikin fitattun waƙoƙin Salma Saeed Mailambu guda 20, waɗanda aka tattara aka mayar da su cikin littafi domin bunƙasa harkar adabi da kuma adana waƙoƙin Hausa na wannan zamani.
Littafin mai shafuka 58 ya samu sharhi daga Dakta Murtala Uba na Jami’ar Bayero da ke Kano, yayin da Dakta Aisha Mai Mota ta kasance mai ta’aliki a wajen gabatar da shi.

Haka kuma, littafin ya samu dubawa da gyare-gyare daga masana harkar adabi, ciki har da Dakta Ibrahim Sheme, PhD, na Jami’ar Karatu Daga Gida ta Ƙasa (NOUN), yayin da Dakta Mujahid daga Jami’ar Jihar Kaduna ya gabatar da jawabin ƙarfafa gwiwa.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai Farfesa Abdullahi Uba Adamu, Malam Ibrahim Khalil, Hon. Sani Hamza Rimaye, ɗan majalisar dokokin Jihar Katsina, Alhaji Abdul Amart, da Malam Ashafa Murnai, wanda ya wakilci Dakta Ibrahim Sheme, da kuma mawaki kuma Basarake Dr. Aminu Ladan Abubakar Ala.

By ukarofi

Leave a Reply