Yadda aka gudanar da bajekolin finafinai na KILAF 2023 a Kano

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

A ranar Talatar makon jiya  ne aka fara bikin kalankuwa ko bajekoli na Afirka mai suna ‘Kano Indigenous Languages of  Africa Film  Market and Festival’, wato KILAF a taƙaice da a ka yi wa na bana laƙabi da ‘KILAF AWARD 2023’, wanda kuma shi ne karo na shida da aka gudanar tun daga lokacin da aka fara shi a 2018.

An kammala taron a ranar Asabar 26 ga Nuwamba, 2023, da bikin bayar da kyautuka na gasa da a ka yi na harsunan Afirka bayan kwanaki biyar da aka kwashe ana gudanar da bikin wanda na farko aka fara da liyafar cin abinci ta yi wa baƙin maraba wanda manyan mutane suka halarta a otal ɗin Brustal da ke cibiyar gidan gona a kan titin Guda Abdullahi.

A Rranar Laraba kuma aka buɗe taron bita da ake yi duk shekara wadda a wannan shekarar aka yi wa bitar laƙabi da cewa, ‘ya za a yi a warware katutu na mulkin mallaka da yake zukatan ‘yan Afirka’ wanda kuma a lokacin taron an gabatar da takardu wajen guda goma sha huɗu daga mutane da suka fito daga ƙasashe wajen biyar kuma an shirya bitar tare da haɗin gwiwar tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero a harabar makarantar aka yi na tsawon kwana biyu.

Bayan wannan an shirya wata bita ta ilmintar da jarumai yadda za su inganta harkar wasan kwaikwayon su in da aka gayyato masa a kan harkar fim suka bayar da horon wanda shi kuma aka shafe tsawon kwanaki uku ana yi. Kuma a daidai lokacin da ake hosarwar an yi bajekolin kayayyakin al’adu da kayan gargajiya  da abincin mu na na gargajiya inda duk wanda ya yi rajista ya shiga taron ake ba shi abincin don ya ɗanɗana irin abincin da ake da shi na gargajiya har ma da kayan sha irin su zobo da sauran su wanda ya zama duk wani abinci da aka ci a wajen na gargajiya ne aka bayar saboda a nuna Kano akwai abinci na gargajiya.

Bayan an shafe kwanaki uku ana gudanar da wannan sai kuma aka ware ranar Asabar domin zagayawa da baqin da suka zo don a nuna musu wuraren tarihi da Kano take da shi. Sai kuma da daddare aka yi taron bikin karramawa da kuma bada kyautuka ga fitattaun mutane tare da finafinan da suka shiga gasar a wannan shekarar wanda kuma shi ne ya zamo taron na ƙarshe da aka rufe bikin da shi
Finafinan da suka yi nasara a gasar KILAF 2023 su ne kamar haka:

Gwarzon labari: ‘Ngoda’
Gwarzon tsara wajen aiki: ‘Herds men’
Gwarzon Kwalliya: ‘Ngoda’ 
Gwarzon tsara hotuna: ‘Kikum Spiirit’
Gwarzon  sauti: ‘Ngoda’ 
Gwarzon tace labari: ‘Enonil’
Gwarzon Jarumi: Adam Juma da fim ɗin ‘Eonii’
Gwarzon Jaruma: Radeeya Jibril da fim din ‘Eonii’
Gwarzon Jarumi mai tasowa: Taurai Kawara da fim ɗin ‘Ngoda’ 
Gwarzon Darakta: Hafizu Bello da fim ɗin ‘Aisha’
Gwarzon  fim din tarihi: ‘Lobola’
Gwarzon gajeren fim: ‘Deor ward’
Gwarzon harshen gida na Afirka: ‘Aisha’ 
Gwarzon fasalin fim mafi  kyau: ‘Ngoda’
Gwarzon hoto: ‘Ngoda’

A taƙaice dai fim ɗin ‘Ngoda’ na Ƙasar Zimbabwe shi ne ya yi fice a cikin dukkan matakai na gasar KILAF2023 wanda ya yi nasara a matakai guda bakwai.

Hakan ya nuna tsarin da a ka bi wajen fitar da finafanan  ba a yi son zuciya ba, kawai dai an nuna tsatsar cancanta.

By Editor