Tinubu ya yi matuƙar damuwa kan iftila’in Tudun Biri – Malagi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nuna damuwa matuƙa kan iftila’in da ya auku a yankin Tudun Biri, Jihar Kaduna inda sojoji suka jefa wa masu taron maulidi bom bisa kuskure.

Hadimin Ministan, Rabiu Ibrahim, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin cewa, Malagi ya bayyana haka ne a wajen taron Babban Kwamitin Shugabancin Jama’atu Nasril Islam (JNI) da ya gudana ran Litinin a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ministan ya nuna godiyar gwamnatin ga sarakunan gargajiya da shugabannin addini bisa ƙoƙarin da suke wajen kwantar da hankulan jama’a dangane da harin Tudun Biri.

“….cike da alhini nake miƙa saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da musulman da suka mutu a Tudun Biri, Jihar Kaduna, wanda hakan ya faru ne bisa kuskuren da sojoji suka yi wajen kai farmaki.

“Muna roƙon Allah Subhanahu Wata’ala Ya ba mu haƙuri da juriyar abin baƙin cikin da ya faru, kana Ya bai wa waɗanda suka tagayyara lafiya, amin.”

Ministan Ya ƙara da cewa, “Shugaba Tinubu ya bayyana damuwar da yakan ji duk lokacin da aka samu bom ya yi ɓarna, don haka ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

“Ya kuma buƙaci jama’a a kwantar da hankula sannan hukumomi su ci gaba da gudanar da bincike kan iftila’in.”

Malagi ya kuma taɓo batun yadda Shugaban Ƙasar ya tura tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, domin jajanta wa al’ummar yankin Tudun Biri da ma gwamnatin Jihar.

By Editor