Yadda bankunan Nijeriya ba sa iya taɓuka komai yayin da kuɗin masu ajiya suka yi ɓatan dabo

Spread the love

Daga AMINA YUSUF ALI

“Abin ya sha kanmu, je ki CBN ki kai kukanki!” Wannan ita ce amsar da mahukuntan wani banki suka ba wa wata mata bayan da kuɗaɗenta har Naira 91,900 suka ɓace ɓat, daga asusun ajiyarta na bankin.

Ita dai wannan mata mai suna Rebecca Jolaoso, ‘yar kasuwa ce ‘yar asalin garin Ibadan.

Rebecca ta zayyyana yadda Bankin Polaris ya kasa yi mata wani kataɓus bayan Naira 91,900 zuwet ta fita daga asusun ajiyarta na bankin Polaris ba bisa ƙa’ida ba. Duk kuwa tana tare da katin cirar kuɗinta a tare da ita.

Rebecca ta bayyana cewa, ranar 20 ga watan Agusta ne dai ta samu ƙararrawar sanarwar cire Naira 91,900 daga asusunta. Kuma a lokacin da al’amarin ya faru ta bayyana cewa, ta cika da mamaki sosai domin a lokacin da abin ya faru, wayar salularta da kuma katin cirar kuɗinta duk suna tare da ita.

Jolaoso ta bayyana cewa, ganin haka ya sa ta je bankin don gabatar da ƙorafinta, sai bankin ya umarce ta da ta kira layin taimako na bankin. Inda jami’an kula da masu ajiyar suka yi mata alƙawarin za su yi bincike kuma su warware matsalar.

A cewar ta, ta yi jewar zuwa Bankin amma tsahon watanni uku matsalarsa ta qi warwaruwa. Daga bisani kuma bankin ya umarce ta da ta je Babban Bankin Nijeriya, CBN don ba da ƙorafinta domin abin ya sha kansu.

Ba a kan Rebecca wannan abin ya soma faruwa ba. Irin waɗannan kesa-kesai sun zama ruwan dare a bankunan Nijeriya.

Ina mafita a kan irin waɗannan abubuwa. Ya kamata bankuna su ɗauki matakin tsare wa masu ajiyarsu dukiyoyinsu domin yardar da suka ba su.

By Editor