DA ƊUMI-ƊUMI: Sai da Lambar ‘Yan Ƙasa za a riƙa hawa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da samar da tsarin yin amfani da Lambar ‘Yan Ƙasa (NIN) ga kowane fasinja dake sha’awar hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna.

Ministan Sufuri na Nijeriya, Mu’azu Jaji Sambo, ne ya bayyana hakan a yau Lahadi lokacin da ya ke zagayawa da ‘yan jarida, ciki har da Blueprint Manhaja, don duba irin shirye-shiryen da aka yi, don dawo da zirga-zirgar, wacce aka dakatar da ita ranar 28 ga Maris, 2022, sakamakon harin ta’addanci da aka kai masa har aka kashe wasu fasinjoji kuma aka yi awon gaba da wasu.

Ministan ya ƙara da cewa, a cikin makon nan da ake shiga ne za a fara sayar da tikitin jirgin makonni bayan sako dukkan fasinjojin da aka yi garkuwa da su.