Najeriya na gab da rasa jiragen saman da Shugaban Ƙasa ke amfani da su saboda tarin bashi – Rahoto

Daga WAKILINMU

Alamu masu ƙarfi sun nuna Najeriya na gab da rasa jiragen saman da Shugaban Ƙasa ke amfani da su saboda bashin da ya yi mata katutu.

Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ranar Lahadi ya nuna hakan na shirin faruwa ne saboda bashin da wasu kamfanoni ke bin ƙasar wanda ta ƙagara biya.

Jiragen da lamarin ya shafa da su ake amfanin wajen jigilar Shugaban Ƙasa da mataimakinsa da iyalansu haɗi da manya jami’an gwamnatin ƙasar.

Kwamanda mai kula da jiragen, Air Vice Marshal Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake kare kasafinsa a Majalisar Tarayya.

Kazalika, jami’in ya yi ƙorafin biliyan N1.5 aka ware daga biliyan N4.5 ɗin da ya nema don kula da jiragen.

Tun daga shekarar 2016, Shugaba Muhammadu Buhari ya ware biliyan N81.80 don kula da waɗannan jiragen da yake amfani da su wajen zirga-zirga a sassan duniya.

Kuma tun bayan da Buharin ya karɓi mulki, Fadar Shugaban Ƙasa ta keɓe jirage 10 don amfanin Shugaban Ƙasa.