A hau jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna gaba-gaɗi, ba fargaba, inji Ministan Sufuri

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Ministan Sufurin Nijeriya, Mu’azu Jaji Sambo, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya masu sha’awar hawa jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna da su yi shirin hawa gaba-gaɗi ba tare da wata fargaba ba, yana mai cewa, an yi kyakkyawan tanadi, don kare rayuka da lafiyar fasinjoji a yayin da zirga-zirgar jingin ta dawo.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau Lahadi, ciki har da Blueprint Manhaja, yayin duba irin shirin da Gwamnatin Tarayya ta yi na sake buɗe zirga-zirgar jiragen ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna.

“Ina so na tabbatar wa duk wanda zai shiga jirgin nan, wallahi ya shiga jirgin nan kai-tsaye ba tare da wata tantana ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, akwai tsare-tsare na tsaro waɗanda suke a fili da na ɓoye. Don haka babu sauran fargabar tsaro a jirgin.

A yayin da yake bayar da tabbacin tanadin tsaron da aka yi wa zirga-zirgar jirgin, don rayukan fasinjojinsa, ya ce, “alhamdulillahi, tunda ka gan mu a nan, ka san cewa, mun yi iya abinda ɗan adam zai iya yi. Sai mu cigaba da roƙon Allah Ya ƙara tsare mu, Allah Ya tsare ƙasarmu, Allah Ya ba mu sa’a mu miƙa mulki shekara mai zuwa lafiya.”

Lokacin da ya ke amsa tambaya kan tanadin da aka yi na shiga jirgin, ya ce, yanzu sai da Lambar ‘Yan Ƙasa za a riƙa sayen tikiti.

Don haka ya yi ƙarin haske kan batun ‘yan ƙasar waje, waɗanda ba su da lambar, sai ya ce, “Bari na gaya maka wani abu ɗaya… Yawancin waɗanda suke da hannu a irin waɗannan tashe-tashen hankulan, ai ‘yan ƙasashen waje ne,” inji Sambo.

Sai dai a cigaba da tattaunawar ya ƙara da cewa, Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Nijeriya ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Rijistar ‘Yan Ƙasa, wacce ta ke da tanadi na yi wa ‘yan ƙasashen waje rijistar wucingadi a lokacin zamansu cikin Nijeriya, yana mai cewa, hukumar za ta buɗe ƙananan ofisoshinta a tashoshin jiragen ƙasa na Abuja da Kaduna, don tabbatar da aikin tantance fasinjojin ya tafi daidai.

A ƙarshe, Minista Sambo ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin tsaronsu a cikin jiragen.