Sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a: Sama da kashi 80 na masu amsa tambaya a duniya na kiran da a kauce wa samun ƙaruwar sabbin masu harbuwa da cutar COVID-19

Daga CMG Hausa

A halin yanzu dai ana ci gaba da samun ɓullar cutar numfashi ta COVID-19 a faɗin duniya.

Tun daga farkon wannan shekara, adadin waɗanda suka mutu a duk duniya sakamakon cutar ya zarce miliyan ɗaya, kuma har yanzu kwayar cutar tana ci gaba da canzawa.

A ‘yan kwanakin da suka gabata, sashen CGTN na babban rukunin gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin wato CMG, ya ƙaddamar da wani bincike tsakanin masu amfani da yanar gizo a duk faɗin duniya, wanda sakamakon sa ya nuna cewa, sama da kashi 60% (60.44%) na waɗanda suka amsa tambayoyi, sun damu matuƙa game da illar da cutar ke haifarwa ga lafiyar ɗan adam a dogon lokaci.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cewa, ɓarkewar cutar na ci gaba da zama “lamarin gaggawa ga lafiyar jama’a da ke addabar ƙasashen duniya”.

Hukumar ta kuma ba da shawara ga ƙasashe daban daban, da su ci gaba da sanya ido kan cutar, tare da sabunta shirye-shiryensu na tinkarar annobar.

Dangane da hakan, kashi 85.4% na waɗanda suka amsa tambayoyin sun yi imanin cewa, ya kamata a ɗauki matakan hana kamuwa da cutar, kuma kashi 8.3% ne kaɗai suka nuna rashin damuwa dangane da halin da ake ciki.

Waɗanda aka zanta da su, ba su yi watsi da batun tinkarar annobar yadda ya kamata, kamar yadda kafafen yada labarai na ƙasashen yamma ke tallatawa ba.

Akasin hakan ma, yayin da ra’ayin “yin watsi da” rigakafin cutar ke ƙara ta’azzara, da hadarin canzawa, da yaɗuwar annobar, a daya hannu cutar na ci gaba da yin illa ga al’umma a fannonin ƙaruwar nau’o’in ta da ake da su, ta fuskar kayan aikin likitanci da karancin ma’aikata.

Ƙasashen da suka ɗauki matakan ko-in-kula game da rigakafin kamuwa da cutar a yanzu ba su ga ta zama ba, balle su kai ga cimma nasara a kwance.

Mai fassara: Bilkisu Xin