Daga CMG HAUSA
Ƙasar Sin na ƙara faɗaɗa kafa turakun samar da nau’o’in makamashi da ake iya sabunta amfani da su, tun daga farkon shekarar nan ta bana, yayin da mahukuntan ƙasar ke yunkurin wanzar da ci gaba, ba tare da gurbata muhalli ba.
Alƙaluman hukumar kula da makamashi ta ƙasar sun nuna cewa, ya zuwa ƙarshen watan Oktoba da ya shuɗe, Sin ta kafa jimillar cibiyoyin samar da lantarki da ya kai kusan kilowatt biliyan 2.5, adadin da ya nuna ƙaruwar kaso 8.3 bisa dari a shekara ɗaya.
Cikin jimillar, adadin lantarki ta ƙarfin iska ya ƙaru da kaso 16.6 bisa dari, daga adadin da ake da shi a bara zuwa kilowatt miliyan 350, yayin da lantarki ta hasken rana ya kai kilowatt miliyan 360, adadin da ya ƙaru da kaso 29.2 bisa ɗari a shekara.
A bana, ƙasar Sin na ƙara azama wajen bunƙasa zuba jari a fannin makamashi da ake iya sabuntawa, inda aka gina manyan filaye masu ɗauke da allunan tattara hasken rana, da turakun samar da lantarki daga iska, musamman a yankunan hamada.
Mai fassara: Saminu Alhassan
